ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Neja: An Ceto Mutane 7 Da Suka Makale Wajen Hakar Ma’adanai

by Sadiq
2 years ago
Hakar Ma'adinai

Gwamnatin tarayya ta ceto wasu mutane bakwai da suka makale a wani wajen hakar ma’adanai a yankin Galadima Kogo da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Ministan ma’adanai, Dele Alake ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori ya fitar ranar Talata a Abuja.

  • ‘Yan ta’adda 176 Sun Mika Wuya, An Cafke 57 A Tafkin Chadi – MNJTF
  • Hajj 2024: Jihar Kaduna Ta Kammala Jigilar Maniyyata Fiye Da 4,000 Zuwa Saudiyya 

Ya ce tuni aka tura masu bayar da agaji zuwa wajen da lamarin ya faru, inda ya kara da cewa ana aikin ceton tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai.

ADVERTISEMENT

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa mutane 30 ne, suka makale cikin ramin da ake hakar ma’adanai da kamfanin African Minerals and Logistics Ltd ke aiki.

NAN ya kara da cewa, Alhaji Abdullahi Arah, Darakta-Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Neja (NSEMA), ya ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.

LABARAI MASU NASABA

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

Tinubu Da Shettima Duk Suna Kasar Waje, Wa Ke Shugabantar Nijeriya Yanzu? In Ji Melaye

Ministan ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ya nuna yadda ta himmatu wajen ganin an dakile asarar rayuka, da kuma ceto wadanda suka makale.

“Da samun labarin faruwar lamarin, sai muka tura jami’an kula da ma’adanai na tarayya (FMO) da jami’an hukumar binciken ma’adanai wajen.

“Tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai, mun ceto mutane bakwai da suka makale. Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wajen,” in ji shi.

Ya kuma bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar yin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.

MASU ALAKA

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 
Manyan Labarai

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

September 21, 2026
Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Manyan Labarai

Tinubu Da Shettima Duk Suna Kasar Waje, Wa Ke Shugabantar Nijeriya Yanzu? In Ji Melaye

September 21, 2026
Ƴansanda Da Sojoji Sun Ƙara Tsaurara Tsaro A Wuraren Da Ake Zargin Za A Kai Hari
Manyan Labarai

Ƴansanda Da Sojoji Sun Ƙara Tsaurara Tsaro A Wuraren Da Ake Zargin Za A Kai Hari

September 21, 2026
Next Post
Sanata Yari Ya Samar Da Taki Ga Manoman Zamfara A Kan Naira 20,000

Sanata Yari Ya Samar Da Taki Ga Manoman Zamfara A Kan Naira 20,000

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

September 21, 2026
Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

September 21, 2026
Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

September 21, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

September 21, 2026
Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

September 21, 2026
Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

September 21, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

September 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.