Kungiyar Mata Masu Noma ta Nijeriya (NAWIA) reshen Zamfara ta tallafa wa mata 114 da kungiyoyin mata 6 da kayan aikin gona a Zamfara.
Shugabar Kungiyar NAWIA ta jihar, Hajiya Shemau Nalado ce ta raba kayan tallafin ga mata manoma a taron tunawa da ranar abinci ta duniya da aka gudanar a Gusau, ranar Alhamis 16 ga watan Oktoba, 2025.
- Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa
- Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC
Nalado ta bai wa mata manoma 70 kayan shuka iri na Shinkafa da na waken soya, takin zamani, maganin ciyawa da kuma maganin kwari.
Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.
Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.
Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.
Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.
Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA sun hada da Zamfara Chambers of Commerce, ACRESAL, NG-CARES, LIPAN, LP PRESS da kuma Nigeria Export Promotion Council (NEPC).