An ware ranar 27 ga watan Yulin kowace shekara ne don wayar da kan jama’a game da haɗari da kuma hanyoyin kauce ma kamuwa da mummunar cutar nan ta Kansar Kai da Maƙogwaro.
Wannan wayar da kai da masana cutar ta duniya ta shirya a kowace irin wannan rana, ta zama wajibi ne bisa la’akari da cewa ita wannan cuta ta fi sauƙin magani, tare da kawar da ita daga jikin mutum ne kawai idan an gano ta da wuri, amma idan abin ya girma, har ta fantsama, to tana da wuyar magani.
- Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
- Nijeriya Da Indiya Za Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi
Hakan ne ta sa aka zabi wannan rana domin a wayar wa da jama’a kai game da hanyoyin da za su bi wajen kare kan su daga kamuwa da cutar, wanda hakan zai taimaka wajen rage yaɗuwar ta.
Waɗannan bayanai duk suna ƙunshe ne a cikin jawaban da aka gudanar a gangamin wayar da kai game da wannan cuta, wanda ya gudana a Kaduna.
Lokacin da ta ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wannan gangami, Dr. Maimuna Lawal Garba, ƙwararriyar Likita a fannin hanci, kunni da maƙogwaro, ta fara bayanin ta ne da bayyana abubuwan da suke haddasa wannan cuta ta Kansar Maƙogwaro.
Ta ce, “Muna bai wa mutane shawara su kiyayi shan tabar sigari, barasa (giya). Haka kuma akwai yanayin aikin mutane, misali, masu aiki a wurin yankan katako, wannan ƙurar ta katako tana daga cikin abubuwan da za su iya sabbaba ma mutum kamuwa da wannan cuta.
“Haka kuma akwai (radiation), na’urar haske, idan ya shiga ƙwaƙwalwa zai iya haifar da wannan cuta. Haka kuma akwai yawan shekaru na tsufa, akwai kuma ƙwayar cutar HPF, ita ma tana sabbaba kamuwa da wannan cuta. Haka kuma idan mutum yana da gadon wannan cuta, shi ma zai iya zama musabbabin kamuwa.”
Shi kuwa Dr. Muhammad Sani, wanda ya ke shi ma Likita ne a wannan fanni na Hanci, Kunni da Maƙogwaro, cikin jawabin sa, ya ce, abin takaici ne ganin cewa wannan cuta ta Kansar Hanci, Kunne da Maƙogwaro tana ƙara yaɗuwa a duniya, musamman yankin Afrika, wanda kuma Nijeriya na ciki.
Da ya ke ƙarin haske, Dr. Usman Ibrahim Sani, wanda shi ma ƙwararren Likita ne a wannan fanni, ya bayyana cewa ba wai masu shan sigari da giya ne kawai suke kamuwa da wannan cuta ba, “zai iya faruwa da waɗanda ba sa mu’amala da waɗannan abubuawa, amma yana da kyau mutum ya garzaya asibiti tun abin na ɗan ƙarami, ta yadda zai fi sauƙin magancewa,”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp