Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba 1 ga watan Mayu, 2024, a matsayin hutu, domin bikin ranar ma’aikata.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
- Karancin Mai: Majalisa Ta Gayyaci Ministan Man Fetur
- Dan Majalisa Ya Kaddamar Da Ajujuwa 3 A Firamare A Adamawa
“Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 1 ga watan Mayu, a matsayin hutu domin bikin ranar ma’aikata,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta jaddada bukatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkan matakai.
Kazalika, ta bukaci ma’aikata su zage da damtse da himma wajen sake gina Nijeriya.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da kokawa da karancin man fetur tare da tsadarsa.