Ana gudanar da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin wato Canton Fair a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin. A yayin bikin baje kolin, na bi wani dan kasuwa daga Najeriya Dawud Jidda Jidda don fahimtar yadda zai gudanar da aikin sayayya a wannan biki. Dawud ya kai ni wani shago mai samar da allunan tattara hasken rana don samar da wutar lantarki, inda ya ce: “Allunan da kamfanonin Sin suka samar na da inganci matuka, kuma ‘yan kasuwar Najeriya na matukar sonsu. Ban da hajoji masu amfani da makamashi mai tsabta, suna kuma gamsuwa da kayayyakin lanturoni da Sin ta samar. Na shafe tsawon shekaru 3 a nan kasar Sin, kuma na halarci bikin baje kolin Canton Fair sau 3. A wannan karo, abokaina daga Najeriya sun ba ni odar sayen hajoji daga kasar Sin, kuma wannan biki ya zama dandali mafi kyau wajen zabar hajojin.”
Ban da wannan kuma, Dawud ya gaya min cewa, ya zabi kamfanoni 3 masu inganci, kuma abu na gaba shi ne, tattauna farashi.
- Hungary Na Sa Ran Ziyarar Xi Za Ta Bude Sabon Babi A Dangantakarta Da Sin
- Shugaban Serbia: Zan Rubuta Wani Littafi Don Tunawa Da Hulda Ta Da Xi Jinping
A yini na biyu, ya kai ni dakin ajiye hajoji wanda ya kafa bisa hadin gwiwa da ‘yan kasuwa Sinawa, inda ake kokarin kunshe hajoji da sanya su cikin akwatunan da za a yi jigilarsu ciki, kana ana gudanar da ayyuka bisa tsari mai kyau. Ya kara da cewa, ana jigilar hajoji ta jirgin ruwa a kalla sau 2 ko 3 a ko wane mako, kuma ana iya tattara mabambanta hajoji cikin akwati daya. Har ila yau, ya ce a baya, jigilar kayayyaki zuwa Nijeriya kan dauki watanni 6, amma yanzu hajoji suna isa tashar jirgin ruwa a Najeriya, cikin watanni 2 ko 3.
Kazalika, Dawud ya ce, yana zabar nagartattun hajoji a Canton Fair, da gudanar da cinikayya ta hanyar hadin gwiwa da Sinawa abokansa, kuma gwamnatin Sin ta samar da manufofin kwastam masu kyau. Ya ce bunkasuwar Sin na ba shi zarafi mai kyau wajen gudanar da harkokin cinikayya, inda ya bayyana birnin Guangzhou a matsayin mafarin ciniki, kana mafarin zaman rayuwa mai inganci. (Mai Zane da rubutu: MINA)