Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice (NIS) reshen Jihar Ribas, James Sunday, ya gargadi jami’a hukumar reshen jihar, kan mahimmancin tsaftace muhallin aikinsu da sauran wurin zama.
James ya yi wannan gargadin ne don zagayowar ranar bikin tsaftar muhalli ta duniya, inda ya nanata cewa, hukumar ba za ta lumunci duk wani jami’in da ya shiga aikin na kula da shige da fice, ya kasance yana barin muhallansu ko tituna ko kuma gun aikinsu ba a tsaftace ba.
A cewarsa, dole ne mu koyi darasin tsaftace muhallanmu da kuma guje wa jefar da leda da kuma robobin da aka sha kayan zaki a kan tituna ko a inda bai kamata ba.
Ya yi nuni da cewa, ana gane tsaftar jami’i ne ta hanyar idan ya ci wani abincin da aka zuba a cikin wata roba ko kuma wani lemon roba, sannan kuma ya saka robar da ya ci abincin ko lemon na roba a inda ya dace, musamman don gudan tara datti da kuma janyo kwari kamar irinsu kyankyasai da sauransu.
Ya yi nuni da cewa, lafiya jari ce, a saboda haka ya zama waji mu san yadda za mu kare kawunanmu daga kamuwa da cututtuka.
Kwanturolan ya kara da cewa, irin muhallin da muke a zaune, shi ne ke nunawa a zahri irin da’a da kuma halinmu, a saboda haka, ya zama waji mu kasance a kan gaba wajen tabbatar da tsaftar muhallanmu da kuma a gun da muke gudanar da ayyukan mu.
James ya bayyana cewa, “ina son in yi amfani da wannan damar domin in ta ya ku murnar zagayowar ranar ta tsaftace muhalli ta duniya.”