Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya, wadda aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sha alwashin komawa bakin aikinta na majalisa a ranar Talata mai zuwa, bayan da wata kotu ta bayar da umarnin majalisar ta janye dakatarwar da aka yi mata na tsawon watanni shida.
Sanatar ta bayyana hakan ga magoya bayanta cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.
- Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
- Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Natasha A Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Akpabio Da Yahaya Bello
Ta yi godiya ga magoya bayanta bisa hukuncin kotu da ya tabbatar da matsayin ta a Majalisar Dattawa.
Ta ce, “Na gode da goyon bayan ku. Ina farin ciki da nasarar da muka samu yau. Za mu koma Majalisar Dattawa a ranar Talata da ikon Allah.”
A wani labari makamancin wannan, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ci tarar Akpoti-Uduaghan naira miliyan biyar a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan da ta same ta da laifin raina kotu saboda wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook wanda ya saɓa da umarnin kotu da ta bayar a baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp