• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Duniya

Kamar yadda duk mai bibiyar al’amuran dake wakana a duniya ya kwana da sani, an gudanar da bikin ranar tattaunawa tsakanin wayewar kan kasa da kasa ta MDD a karo na farko a Talata da ta gabata, kuma hankulan duniya sun karkata ga wannan manufa ta yunkurin dinke duniya waje guda, wanda masharhanta da dama ke kallo a matsayin yunkuri na kusanto da sassan wayewar kai na kasashen duniya daban daban, musamman a gabar nan da ake ta fuskantar rarrabuwa, da rashin fahimtar juna, da tashe-tashen hankula dake neman zama ruwan dare.

Idan mun waiwayi tarihi, za mu ga cewa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da mahangar ingiza wayewar kan daukacin sassan kasa da kasa ta GCI cikin watan Maris na shekarar 2023, inda manufar ta fadada zuwa muhimmin ginshiki na cudanyar Sin da sauran sassan duniya.

  • Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu
  • Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane

Wannan manufa tana gudana kafada-da-kafada da takwarorinta, irin su shawarar samar da ci gaban daukacin duniya ko GDI, da ta inganta tsaron duniya ko GSI. Hadakar wadannan manufofi uku, ta samar da wata kyakkyawar alkibla ta gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama.

Idan mun nazarci manufar nan ta tattaunawa tsakanin wayewar kan kasa da kasa ta MDD, wadda aka yi bikinta a baya bayan nan, za mu ga cewa an gina ta ne kan ginshikai hudu, wato martaba bambance-bambancen wayewar kai, da yayata bukatar gina akidun bai daya na bil’adama, da wanzar da zaman lafiya, ci gaba, adalci, gaskiya, dimokaradiyya, da yanci. Sauran su ne dagewa wajen gadarwa, da kirkire-kirkire a fannin kare wayewar kan bil’adama, da kuma tallafawa ingantaccen salon hadin gwiwa da musaya tsakanin al’ummun sassan kasa da kasa.

Wadannan ginshikai sun kara yayata akidun MDD, na kira da a hada kai tare da dukkanin bambance-bambance, da wanzar da zaman lafiya da daidaito tsakanin al’ummun duniya. Manufar wayewar kan daukacin sassan kasa da kasa ta GCI, ba wai tana kokarin samar da wani salo daya tilo da za a tursasa biyayyarsa ba ne, maimakon haka, tana fatan ganin an rungumi dukkanin nau’o’in wayewar kai ne, ta yadda za su samar da alfanu, da damar koyi daga juna.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

A wannan lokaci da wasu sassa ke kafa shingaye, GCI na gina gadoji. Manufar na kuma karfafa gwiwar tattaunawa, da gudanar da shawarwari tsakanin sassan duniya masu bambance-bambance, ta yadda za a kafa managarcin tsarin hadin kan bil’adama mai dorewa. GCI da ranar tattaunawa tsakanin wayewar kan kasa da kasa ta MDD, za su kara zamewa duniya muhimman manufofi na “tafiya tare a tsira tare”!(Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post
De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City

De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.