Shugaban Kasa Bola Tinubu zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya zuwa birnin Bissau na Kasar Guinea-Bissau domin bikin cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngalale ya fitar, shugaba Tinubu zai isa birnin Bissau a ranar Alhamis domin bikin, wanda shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo zai shirya.
- Ribadu Ya Bukaci NLC Ta Janye Yajin Aiki, Ya Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Da Aka Yi Wa Ajaero
- Matar Aure Ta Kone Gidan Mijinta Saboda Ya Ki Sakin Ta
Guinea-Bissau ta cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai a ranar 24 ga watan Satumba, 2023, amma gwamnatin kasar ta dage bikin ranar zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023.
A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaba Tinubu zai dawo Nijeriya.