Ƴan wasan gefen Barcelona, Raphinha da Lamine Yamal, sun jagoranci ƙungiyar zuwa nasarar 2–0 a kan Villarreal a ranar Lahadi, lamarin da ya bai wa Barcelona damar yin tazarar maki huɗu a saman teburin La Liga. Nasarar ta kuma tabbatar da cigaban Barcelona a matsayin jagorar gasar a kakar bana.
Ɗan wasan Brazil, Raphinha, ne ya fara zura ƙwallo bayan ya samu bugun daga kai sai mai tsaron gida tun a farkon wasan, wanda ya kuma sura shi kai tsaye. Kafin a tafi hutun rabin lokaci, Villarreal ta rage zuwa ’yan wasa 10 bayan da Renato Veiga ya samu jan kati sakamakon keta ka’ida kan matashin ɗan wasa Lamine Yamal.
A tsakiyar zagaye na biyu, Yamal mai shekaru 18 ya zura ƙwallo ta biyu, hakan yana tabbatar da nasarar Barcelona da kuma dawo da tazarar da take da ita a kan Real Madrid wadda ke matsayi na biyu. Wannan nasara ita ce ta takwas a jere da Barcelona ta samu a gasar laliga a ƙarƙashin koci Hansi Flick.
Duk da shan kashin, Villarreal na ci gaba da zama a matsayi na huɗu, bayan Atletico Madrid ta haura gabanta sakamakon nasarar 3–0 da ta samu a kan Girona tun da farko. Kocin Barcelona, Hansi Flick, ya kare Raphinha kwanan nan bayan rashin saka sunansa a jerin ’yan wasan FIFA The Best, kuma ɗan wasan ya mayar da martani da gagarumin bajinta a wannan wasa.
An buga wasan ne a filin Estadio de la Cerámica na Villarreal, bayan da La Liga ta janye shirin kai wasan zuwa Amurka. Raphinha ya nuna ƙwazo da himma a duk tsawon wasan, yana mai sake tabbatar da muhimmancinsa ga Barcelona a fafutukar lashe kofin La Liga na bana.














