Fitaccen mawaki nan mazaunin Jihar Kano, Dauda Kahutu Rarara, ya bukaci babbar kotun Shari’a da ke Jihar Kano da ta yi watsi da karar da aka shigar a gabanta.
Ana zargin Rarara ne kan kin biyan kudi sama da Naira miliyan10 ga wani dan kasuwa mai suna Muhammad Ma’aji.
- Gwamnan Filato Ya Bukaci Jami’an Tsaro Su Kamo Wadanda Suka Kai Hari Wasu Yankunan Jihar
- An Sace Ma’aurata Yayin Da Suke Dawowa Daga Coci A Osun
Kotun wadda mai shari’a Alkali Halhalatul Khuza’i Zakariyya ke jagoranta, na zamanta ne a unguwar Rijiyar Zaki, ta sake dawowa zaman ci gaba da sauraren karar da aka shigar a gabanta.
Lauya mai tsayawa mawakin, G. A. Badawi ya shaida wa kotun cewa, karar ba ta wata madafa saboda haka, ya bukaci kotun ta yi watsi da karar.
Ya ce, sun mika takarda ga wanda ya shigar da karar da kuma ita kotun, amma dan sanda mai gabatar da kara, ya yi ikirarin cewa, sun karbi takardar a kurarren lokaci a yayin da kotun ke shirin zama.
Mai karar Muhammad Ma’aji ya shaida wa kotun cewa, yana da dukkan hujojjin da suke a rubuce domin ya tabbatar da ikirarinsa tun lolacin da ya faro kasuwancin da Rarara a 2021, amma babu wani kudi da ya biya.
Alkali Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ya umarci dan sanda mai gabatar da kara da ya mayar da amsa ga lauyan mai tsayawa wanda ake kara da kuma ita kotun.
Zakariyya ya dage ci gaba da zaman kotun zuwa ranar 12 ga watan Mayun 2003 don ci gaba da sauraron karar.