Tauraron dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford, ya yi hatsarin mota yayin da yake tafiya gida bayan da kungiyarsa ta doke Burnley da ci 1-0 a ranar Asabar.
Rashford, mai shekaru 25, an ba da rahoton cewa Rashford ya yi karo da wata motar yayin da yake barin filin atisaye na United Carrington.
- Hasashe Yadda Wasan Manchester United Da Burnley Zai Kaya
- Hasashen Yadda Wasan Arsenal Da Tottenham Zai Kaya
Rashford ya buga wasa da Burnley, amma ya kasa jefa kwallo a raga a wasan da kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes ya jefa kwallo daya tilo a wasan.
Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun isa wurin inda suka kai daukin gaggawa.
Wata majiya ta ce Rashford ya girgiza amma bai ji rauni ba.
Bruno Fernandes, wanda ya zura kwallo daya tilo a Turf Moor, ya zo kan wurin da lamarin ya faru kuma an yi imanin ya tsaya don ba da taimako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp