• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

byRabilu Sanusi Bena and Sulaiman
4 months ago
Shaba

Tamim Yahuza Abdullahi wanda aka fi sani da (TY) Shaba, a wata tattaunawar da ya yi da jarumar Kannywood Hadiza Gabon a cikin shirinta mai taken “Gabon’s Room Talk Show” ya bayyana abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa ta harkar fim da kuma ta zamowa mawaki wanda ya ce a yanzu ya daina waka sakamakon ganin da yayi cewa ba a nan Allah ya ajiye masa abincinsa ba.

Jarumin wanda ya shafe tsawon lokaci ana damawa da shi a masana’antar Kannywood a matsayin jarumi, mawaki, mai shirya fim da kuma mai daukar nauyi, ya bayyana tarihinsa inda yace shi haifaffen birnin Kano ne, wannan suna na T Y da akasarin mutane sukafi saninshi da shi ya samo asali ne tun daga lokacin kuruciya, na taso a gidanmu na iske yayana yana amfani da sunan D Y ma’ana Dauda Yahuza, hakan ya sa nima na takaita sunana domin ya zama kwatankwacin yadda ake kiran yayana saboda wannan inkiyar tashi a wancan lokacin ta na burgeni inji Tamim.

  • An Daure ‘Yan Nijeriya Uku Shekaru 15 A Bisa Laifin Zamba A Indiya
  • Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

Da yake amsa tambaya akan yadda ya samu Shaba a cikin sunanshi kuwa jarumin ya bayyana cewar sunan Shaba na sameshi ne a lokacin da nake karatu a Federal College Of Education (Technical) Bichi, a wancan lokacin akwai wani mawaki da ake kira Shaba Ranks to da yake ina matukar sha’awar wakokinsa sai ya zamana ina koyi da yanayin yadda yake waka har ma a wani lokaci aka shirya wani taro a makarantar sai na hau dandamali na rera wakokinsa cikin kwarewa.

To bayan na fito ne sai wata abokiyar karatuna ta kirani da wannan suna na SHABa cikin mutane, daga nan tun wancan lokacin sai ya zamana duk wani wanda bai san sunana ba yake kirana da Shaba, dangane da harkar waka kuwa ko da na shigo masana’antar Kannywood ni mawaki ne, domin kuwa na dade ina yin waka duk da cewa dai waka bata karbeni hannu biyu kamar yadda fim ya karbeni ba.

A kowane lokaci ina kiran kai na da wani wanda ko alama bashida basirar waka, hakan ya sa kacokan na hada kayana na koma na cigaba da yin fim a maimakon waka, ya kara da cewa, Shaba kuma ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da suke ci wa masana’antar Kannywood Tuwo a kwarya kama daga rashin samun tallafi daga hukumomi da kuma rashin fadada ilimi a tsakanin jarumai, marubuta da masu shirya fina finan Hausa.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen koyon aiki da kuma tallata hajarsu ga manyan dillalan fim a Duniya wanda ta wannan hanyar sai su samu manyan kudade.

T Y ya cigaba da cewa idan ana maganar masana’antar Kannywood ba haka abin yake ba, domin kuwa a nan yankin sai mai shirya fim ya nemi gida ko kamfanin da zai shirya fim din sa ya rasa, hakan zai sa ya je ya dauki Hotel ko wani gidan haya domin gudanar da aikinsa wanda yace ta haka ne zakaga fina finai suna kamanceceniya da juna saboda kusan komai da komai a waje daya akayi su sakamakon rashin wurare.

Mu a nan arewacin Nijeriya har yanzu ba a daukemu a matsayin wasu da zasu iya kawo cigaba kokuma su samar da aiyuka ga matasa ba, shi yasa ba duk taimako ake mana ba saboda a nasu tunanin babu wani abin cigaba da zamu iya kawowa, yanzu ga misali wanda yafi kowane mutum dukiya a nahiyar Afirika dan arewa ne kuma bahaushe, amma idan yanzu ana son ayi fim wanda za a taka rawar babban mutum kamar Dangote ba lallai bane hakan ta faru.

Saboda ba za a samu isassun manyan gidaje ko manyan motoci da za ayi amfani dasu a fim din ba duk da cewa akwai su da dama, don haka ina kira ga manyan masu kudinmu, mahukuntanmu, sarakuna da gwamnatocinmu su yi kokarin taimakawa wannan masana’antar ta Kannywood da ake shirya fina finai da harshen Hausa ta kowane fanni, hakan zai sa muyi gogayya da takwarorinmu na gida da ma na kasashen waje inji TY Shaba.

Daga karshe ya bukaci matasa da su kasance masu biyayya da hakuri, da kuma jajircewa wajen ganin burikansu sun cika, yace dole ne sai an sha wuya akan sha dadi, kuma duk wanda suka gani a cikin masana’antar Kannywood babu wanda ya shigo a matsayin mai kudi, kowa a talaka ya fara kafin ya zama abinda ya zama, don haka kuma idan kukayi hakuri komai zai zo ya wuce ba tareda wata tangarda ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
Nishadi

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

October 4, 2025
Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa
Nishadi

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

September 28, 2025
Next Post
Wakilin Sin Ya Bayyana Rashin Gamsuwa Da Yadda Amurka Ta Gabatar Da Daftarin Kudurin Kwamitin Sulhu Kan Sudan Ta Kudu

Bangarorin Sudan Da Ke Dauki Ba Dadi Sun Zargi Juna Da Kai Hari Kan Jerin Gwanon Motocin MDD

LABARAI MASU NASABA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version