Shugaban Kungiyar Masu Ilimin Taurari Na Nahiyar Afrika, SHEIKH MUHAJJADINA SANI KANO, ya tattauna da Mataimakin Editanmu, BELLO HAMZA dangane da zanga-zangar ‘yan Nijeriya a kan tsadar rayuwa, inda ya yi has ashen yadda lamarin zai kasance a bisa ma’aunin iliminsu. Ga hirar:
Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu
Sunana Sheikh Muhajjadina Sani Kano, shugaban kungiyar masu ilimin taurarin na Nahiyar Afrika.
Mene ne hasashenku dangane da zanga-zangar da ‘yan Nijeriya ke shirin yi saboda tsadar rayuwa da yunwa da ake fama da ita?
Cikin ikon Allah, dama mun sha fade tun kafin ma a gudanar da zaben shugaban kasa da aka tambaye mu akan mahangarmu kan waye kan gaba wajen nasara. Muka riga muka sanar da cewa shi ne zai yi nasara; sai dai a mulkinsa za a dan sha wahala sosai. Izzar ‘yan kasa za ta tashi. Za a kuma samu fitintinu da rigingimu. Abin da yake mahangarmu ta kowanne fuska daga su ‘yan kasa din da za su yi zanga-zangar da ita gwamnati; mun riga mun yi dogon nazari a kan ita wannan zanga-zanga.
Farko dai bayanin da za mu fara yi kafin mu bayar da shawarwari da kuma hanyar da ya kamata a ce an bi wurin warware wannan matsalar. Wallahi idan aka yi wannan zanga-zangar akwai matsala babba fiye da yadda ake tunani. Gaba daya Nijeriya a duhu take baki daya. Ka da su yarda su bari a yi wannan zanga-zangar. Idan aka yi wannan zanga-zangar, dukkanin wani burinsu su mahukuntan Nijeriya, burinta zai karye baki daya. Ko da su a boye suna da ra’ayin a yi wannan zanga-zangar, suna da wani buri da idan an yi wannan zanga-zangar, to burin nasu ba zai cika ba zai karye. Ba za su taba samun biyan bukata yadda suke so ba. Wannan nazarinmu ne da bincikenmu. Idan suka bari aka gudanar da wannan zanga-zangar, dukkanin wani burinsu ko wani abu da suke so su cimma ko suke hankoro, ko suka ki su bi ma mutane abin da suke so, suka yi wani abu. Gwamnati ta yi wani abu domin tunzura al’umma, na har suka fito suka yi zanga-zanga, to idan suka yi, burinsu ba zai cika ba. Ma’ana akwai wani boyayyen abu da gwamnatin ke son cimma na ko da zanga-zangar aka yi, su sani ba za su samu cikar buri ba.
Nijeriya mun bincika mun gani za a sha wuya, amma ba za ta wargaje ba. Ba za ta zama irin kasashen da ake tunani kamar kasashen da suke ta wannan yaki kamar Falasdin da sauransu, Nijeriya ba za ta zama haka nan ba. Amma za ya koma bayan da tsawon shekaru masu yawa ba ta maye gurbin na abin da ta riga ta rasa ba na komawa baya.
Yanzu Nijeriya ta tashi, a kan wannan kadamin izzar take. A don haka idan za a yi amfani da karfin soja ko jami’an tsaro, a hana ‘yan kasar a ce za a dakile su, to babu wata nasara da za a cimma sai dai illa iyakacin a yi asarar rayuka da dukiyoyi. A zo gaba daya kasar ta shiga halin Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Sannan mun bincika bangaren da gwamnati ke kiran wasu daga cikin manya-manyan Malamai na kasar nan take zama da su, a bincikenmu da nazarinmu, ba mu hana a zauna da Malamai da Sarakuna ba, iyaye ne na al’umma, amma fa su sani wannan kiran na su da suke yi, ba shi zai haifar da maslaha ba. Yau da a ce da muka bincika sai mu ka ga ta hanyar Malaman nan za a samu maslaha na danne abubuwan nan, to da za mu yi bayani cewa Malamai za a nema. Da muka bincika mun gano cewa babu maslaha ta hanyar zama da Malamai da Sarakuna; ba ta wannan hanyar za a samu maslaha da zaman lafiya ba, a takaice ma mu binciken da muka yi, wannan shi yake kara fusata al’umma. Ko suna so ko ba sa so dole sai izzar ‘yan kasa ta tashi ta dan wani lokaci.
A don haka idan har gwamnati ta bari aka yi wannan zanga-zangar a namu binciken, da yiwuwar su rasa mulkin ma. Da yiwuwar hakan ya faru shugaban kasa mai ci yanzu ya rasa mulkin. Sannan idan har aka bari aka yi wannan zanga-zangar, akwai wadansu daga wasu kasashen da wasu daga dan gefe-gefen kasar da za su shigo za su yi amfani da wannan damar su yi wa kasar kaca-kaca. Za su yi amfani da matasan ne su ba su makamai su tunzura su, idan kudi suke so, idan me suke so, su ba su, a dai lalata kasar.
Yau da ake ta jan hankali a kan al’umma ka da a yi zanga-zanga kasa za ta wargaje, shi dama duk wanda ba shi da abincin yau, bai da cin gobe, baida lafiya, shi dama kasa a wargaje take a wurinsa. Idan da shi yake da burin ya busa kaho a tashi duniya zai busa ba ma Nijeriya ba, duk duniyar ma a tashi kowa ya mutu. To wanda bai ci ba yana jin kowa ya mutu yaushe za ka ce da shi wai kasa za ta wargaje? Dama kai ka ke jin dadin kasar. A don haka maslaha, duk abin da ba a cimma burinsa ta maslaha ba, to ta rashin maslaha ba za a cimma wannan burin ba. A don haka a bincikenmu wannan zanga-zangar babu alheri ga gwamnati ko kadan a cikinta.
Amma kuma gaskiya a bincikenmu ta wani gefen, talakawa za su wani ‘yanci da wani cikar burin idan suka yi zanga-zangar. Akwai wani cikar ‘yancin da cikar burin da za su iya samu na wata maslahar saukin rayuwa idan suka yi zanga-zangar, amma ita gwamnati ta sani idan aka yi wannan zanga-zangar ita abin zai fi kwabewa. Su cire son rai da son zuciya, a gyara; ka da a yi. Mu dai a kungiyarmu daga nazarinmu da bincikenmu muna gargadin gwamnatin Nijeriya da kar ta bari a yi wannan zanga-zangar. Amma ta samarwa al’umma zaman lafiya. A bincikenmu da nazarinmu idan har ba a samarwa da al’umma sauki ba, to zanga-zanga ta tabbata sai an yi. Babu wani ja da baya. Babu wani a duniya da zai iya tare wannan zanga-zanga sai ta faru sai an yi ta. Amma za a sha wahala.
Mene ne kiran ku ga talakawan Nijeriya a daidai wannan gabar?
A bincikenmu da na mu hasashen, muna kira ga talakawa cewa; za su samu wani ‘yanci, amma dai ba za su samu biyan bukata dari bisa dari ba. A biyan bukatar da za su samu a kaso goma za su iya samun kaso biyu ko uku. Kaso bakwai bukatarsu ba za ta biya ba. Bukatar gwamnati ita ma ba za ta biya ba. Amma duka yadda za a samu maslaha ga binciken, yana hannun gwamnati. Gwamnati ya kamata ta yi nazari, ta zauna ta yi shawara ta wacce hanya ce za a bi a samar wa wadannan bayin Allah maslaha? Ta wacce hanya ce za a bi a samo wa al’umma ‘yan Nijeriya mafita a samo maslaha. Saboda tabbas maslaha na hannun gwamnati ne ba talakawa ba. Saboda ba maganganu ne da za mu fito mu fadi komai a nan ba. Amma hatta idan gwamnati ba ta san yadda za ta samar wa kanta maslaha ta kuma samar wa al’umma maslaha ba, to don Allah muna so a nemi shawararmu domin mu yi amfani da ainihin wannan ilimi da Allah ya azurta mu da shi mu gaya wa gwamnati ga hanyar da za ta bi ta samu mamakon arzikin da ba ta tunani. Domin gaba daya a binciken, har arzikin da kasar take da shi ya fita. Arzikin da Nijeriya take da shi, da gwamnatin da al’umma da waye, a taurarin arzikin da kasar take da shi baki daya, tun daga samun ‘yancin kai, a arzikin da kasar take da shi kaso dari, da gwamnatin da talakawanta da dukkanin al’ummar kasar da baki ma da suke cin arziki da take da shi, a kaso dari, gaba ki daya, kaso 20 ake yin amfani. Kaso tamanin ma gaba daya hankalinsu bai kai kai ba. Kuma Allah bai ba su iko ba bai bude tunaninsu ba. Saboda karancin amfani da masu ilimin irin wannan na mu. Mun sha fade cewa ya kamata dukkanin matakai na gwamnati, da ofis-ofis na gwamnoni da ‘yan majalisu ya kamata a ce suna tafiya da neman shawarwarin masu wannan ilimin. Kamar yadda kasashen duniya suke amfani da masu irin wannan ilimin domin gudanar da mulkinsu.
Don haka gwamnati ta san me za ta yi bukatar ta ta biya, Duka wannan arziki da muke magana, kaso ashirin ne gwamnati hankalinta ke kai. Rabi ma ba shi ake ci ba wanda Allah ya shimfida wa kasar. Duk a cikin na mu ilimin da binciken, idan gwamnati ta bayar da dama, za mu haska mata wannan kaso tamanin din wanda idan za ta yi amfani da su, kasar idan Allah ya so ya yarda sai an zo gaba daya Nijeriya ta zama irin kasashen duniyar da muke gani muke sha’awa. Sai an rasa wani talaka da zai tashi ya ce ba shi da abin da zai ci ko ba shi da suturar da zai sa. Ko an yi masa haihuwa ba shi da yarda zai yi idan Allah ya so ya yarda. Arzikinmu sai dai wasu kasashen su zo su rika ci. Amma idan har ba ta hanyar masu irin wannan ilimi ba, babu yadda za a yi gwamnatin hankalinta ya karkato wurin. Tabbas rashin amfani da masu ilimin taurari shi ya jefa kasarnan cikin halin da muke ciki. Ni na fada na sake fada.
A karshe me za ku ce?
Muna rokon Allah (SWT) ya kare wannan kasar, ya shiryi shugabanninmu, ya shiryi al’ummar cikinta. Allah ubangiji ya bude zukatan shugabanni da kunuwansu a kan karbar gaskiya. Ya bude zukatan ‘yan kasar da kunnuwansu su zama masu fahimta da gane gaskiya. Allah ubangiji ya shiryar da mu, ya ba mu kariya ya tsare mu. Amma ba mu goyon bayan ko an fito zanga-zanga a fashe kayan wani ko dukiyar wani, duk da dai a bincikenmu idan aka bari aka fara abin nan, to tare shi sai Allah. Idan zai yiwu, ka da ma a bari a yi wannan zanga-zangar. Shi ne gaskiya.
Sannan muna bayar da shawara ga ‘yan kasa da a yi ta addu’a da yi wa kasar nan fatan alheri. A rungumi addu’a. Za mu bayar da addu’ar da kasar ke bukata. Kuma idan an yi ta za a samu biyan bukatar da aka roka. Billahil lazi la’ilaha illahuwa idan ‘yan kasa da hukumomi suka riki wannan addu’a, Billahil lazi la’ilaha illahuwa za a samu biyan bukata da kauce ma musibu idan aka yi wannan addu’a. Bismillahi guda 19, a rike ta ‘yan kasa. Sannan a riki La’ilaha illallahu wahdahu lasharikalahu lahul mulku walahul hamdu wa huwa ala kulli shay’in kadir; kasar nan na bukatar wannan addu’ar kafa 10. Ta wannan sigar muna bai wa ‘yan kasa shawara idan za su roki Allah ta wannan sigar; duk daya idan an fadi La’ilaha illallahu wahdahu lasharikalahu lahul mulku walahul hamdu wa huwa ala kulli shay’in kadir; sai a kai kara a wurin Allah. Haka za a rika yi. Haka Bismillahi 19 a kullum. Mun ba su wannan sirri, bukata za ta biya cikin gaggawa.
A fitar da wannan sirri, wannan La’ilaha illallahu wahdahu lasharikalahu lahul mulku walahul hamdu wa huwa ala kulli shay’in kadir; a fitar da ita, a yi ta a raba ta, a yi ta adadin miliyan tara da dubu dari uku da goma sha uku, a fitar da ita da wannan musibu da tsadar rayuwa da suka addabi mutane a wannan kasa ta mu Nijeriya.