Hukumar dab’i da tace fina finan Hausa na Kannywood ta bayyana takamaiman dalilin da yasa ta dauki matakin dakatar da jarumar Kannywood Khadija Mai Numfashi daga shiga duk wata harka ta Kannywood, da suka hada da rawa da waka da kuma hira da ‘yan jarida da sunan Kannywood.
Abba El Mustapha shugaban hukumar Censorship Board ta jahar Kano ne ya bayyana hakan yayin da yake hira da ‘yan jarida bayan kammala taron da hukumar Hizba ta gayyace su.
- Jiragen Yaki Sun Kashe Shugabannin ‘Yan Ta’adda 3 Da Mayaka 100 A Borno
- Kasar Sin Ta Bukaci Japan Ta Amince Kasashen Duniya Su Sa Ido Kan Yadda Take Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku
El Mustapha ya bayyana cewar ba wani abu ne yasa suka dakatar da Khadija ba sai domin wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta,inda aka ganta ta na rawar rashin da’a tareda da wani namiji a wani gidan rawa.
Abba ya ci gaba da cewar bayan hukumar ta samu wannan bidiyo na Khadija, sun aika mata takardar gayyata domin ta zo su tattauna kuma su yi mata fada a kan abinda suke ganin ta yi ba daidai ba amma sai ta nuna cewar bata a garin Kano a wannan lokacin.
Babban laifin da za ka yi wa hukumar Censorship Board ita ce,mu aika maka takardar gayyata amma ta bijire ka ki zuwa gayyatar da muka yi maka in ji shi.
Saboda haka muka yanke shawarar dakatar da ita daga duk wata sabga ta Kannywood tsawon shekaru biyu domin ta gane kuskuren ta, kuma ya zama izina ga wasu masu irin halinta.
Daga karshe Abba El Mustapha ya kuma nanata kudurin hukumar Censorship Board na tsabtace masana’antar Kannywood daga dukkan wasu masu bata tarbiya da bata wa masana’antar suna a idon Duniya.