Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Taskira. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata mun fara kawo muku tsokaci game da matsalar rashin jituwa a tsakanin ‘yan’uwa na jinni.
Kun ji sharhin da wasu masu bibiyarmu suka yi a makon jiya, yau kuma za mu dora da sharhin da karin wasu suka yi kan wannan lamari da ke matukar ci wa jama’a tuwo a kwarya. Ga abubuwan da suka fada:
Maryam Alhassan Dan’Iya (Maryam Obam) daga Jihar Kaduna:
Gaskiya hakan na faruwa ne a gidan da babu tsayayyun iyaye domin idan akwai jajirtattun iyaye wannan ba zai faru ba, domin tun yara suna kanana ake nuna musu son ‘yan’uwansu, haka kuma suke tasowa da su kuma hakan ya fi faruwa a gidan da iyaye suke nuna ma wani so fiye da sauran yaran. G
laifin iyaye ne domin sune makarantar farko na yaransu, Hakan na haifar da hassada kyashi, kuma wannan abun ba karamin masifa bace domin har yaransu abun zai shafa da jikoki, kuma tarbiyyar yaransu zai zama gashi nan gashi nan ne dai duba da iyayensu suna gaba har suma suna nuna musu su yi koyi dasu tare da tura musu tsanar ‘yan’uwansu.
Gaskiya gujewa aukuwar hakan shine; iyaye su daina nuna wa yaransu bambanci ya zama in za su yi musu abu toh dukansu ne za su yi wa. Shawarar da za a bawa masu wannan matsala ita ce; su ji tsoran Allah su bari domin Allah zai kamasu da rashin zumunci tunda in ana gaba ai babu halin yin zumunci kar mutum ya zo duniya ba ta samu ba lahira bai samu ba Allah yasa mu dace.
Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki) daga Jihar Kano:
Ba komai ke kawo rashin jituwa tsakanin ‘yan’uwa na jini ba face sharrin zuciya da shaidan, mafi yawan lokuta abin da muke tunini akan ‘yan’uwanmu ba haka ba ne sharrin zuciya ne, akwai kuma rashin jituwa da Allah kan saka tsakanin halittarsa.
Mafi yawa iyaye mata ne kan gaba wajen lalata zumunci musamman gida mai tarin iyali, gutsiri tsoma tsakanin mata yana taimakawa sosai wajen haifar da hakan gami da son abin duniya.
Babban matsalar da hakan ka iya haifarwa shi ne lalacewar zumunci tare da rashin hadin kai da kuma bawa makiyanku damar su rusa ku.
Hanyar da za a magance hakan shi ne kai zuciya nesa, kyautata zato ga dan uwanka idan ka ga yayi wani abu da kai a fahimtar ba dai-dai ba ne tare da yi wa juna nasiha kuma kowa ya ji tsoron Allah. Shawara ga wadanda hakan ya riska shi ne; su rike zumunci hannu biyu wanda ya daina kulaka ka kula shi, idan wanda ya daina kulaka ya shiga damuwa ka yi kokari ka yi masa maganin godiyar ko da ba zai gode maka ba.
Rabi’atu Ahmad Mu’azu (Rubby) daga Jihar Jos:
Rarabuwar kai a tsakanin ‘yan’uwa na jini yana samo asali ne daga yawan kananun maganganu dake yawo a tsakaninsu, wasu ma ba iya kanun maganganu ba kyashi da hassada tana taka rawar gani musamman wajan haddasa rarabuwar kai tsakanin ‘yan’uwa na jini, sai ka ga Allah ya ma wata ko wani ni’ima a cikinsu amma wani ko wata na jiny haushin wannan ni’imar yana burin ace ta subuce daga hannunshi ko ita, a gidaje daban-daban za ka samu wadannany matsalolin na faruwa a tsakani.
Kaso tamanin cikin dari laifin iyayen ne saboda sune suke gaba da ‘ya’yansu alhakin tarbiyyar su da ladabtar da su tare da musu nuni da abu mai kyau ko kara kyau yana wuyansu, to sai ka ga an samu wasu iyayen na goyon bayan wasu daga cikin ‘ya’yansu ko kuma suna nuna fifiko a cikin ‘ya’yansu, wannan ma babban abu ne da yake haddasa rarabuwar kai da fituntinu a gidajen mu. Hakan na haifar da matsalolin daban-daban musamman gaba da juna ta yadda za a samu da yawa basa ga maciji da junansu hakan sai yana haifar da mummunar gaba tare da kiyayya mai tsanani idan ba a yi wasa ba ma za ta iya shafar har ‘ya’ya da jikoki.
Za a magance afkuwar hakan ne ta cire kyashi da hassada da kuma son kai a tsakani, tare da nuna soyayya mai tsanani da burin ganin farin cikin juna a ko da yaushe,Y su kuma iyaye su hada kan ‘ya’yansu waje daya ba tare da nuna wariya ko fifiko ba hakan zai sa suma ‘ya’yan su dauki kan su duk daya ne ko da ace suna da bambancin uwa a tsakani.
Duk masu fama da irin matsalar nan su magance ta tun wuri kafin ta zame musu abun da na sani ko kuma ta gagare su ma’ana idan aka fuskanci matsalar ayi kokarin shawo kanta tun da wuri domin ta haifi ɗa mai ido.
Fatima Ibrahim (Muneera) daga Jihar Kano:
Abin da ke kawo rabuwar kawuna tsakanin ‘yan’uwa abu daya ne, fifita wani akan wani da iyaye suke fara yi ko kuma rabuwar iyaye wato uban ya rabu da uwar sai uwar ta dauki wasu haka ma uban ya dauke wasu toh daga nan sai a fara samun matsala ita mahaifiyar tafi fifita na hanun ta haka ma mahaifin ya fi fifita na hanunsa daga nan sai a samu rarrabuwar kawunansu su fara jin haushin junansu ni dai a nawa tunanin kenan.
Laifin daga iyaye ne duka ba wai za a ware guda ace laifin sa bane ko kuma nace lefin uwa ne dan kowace irin tarbiyya daga wurinta take farawa toh duk lokacin da uwa ta fifita daya akan daya toh fa anan ne ‘yan’uwan ke fara jin haushin junansu dan me an yi wa wane abu kaza ni ba a yi min ba ko kuma wane yana magana akan abu sai a yi masa amma ni sai an ga dama ko kuma mkan a aki yi min irin wanan tunaninke sa kan ‘yan’uwa rabuwa.
Matsalar da haka ke haifawar shi ne; rabuwa kan zumunci har girman yara ki ga har girmansu ‘ya’yansu basu wani shaku da junansu ba. Za a iya magance wanan matsalar ne ta wurin iyaye su jajirce wajen su ga basu nuna bambanci tsakanin yaransu ba su yi iya kokari su ga sun hada kan yaransu Allah ya sa mu dace.
Shawarar da zan bawa ‘yan’uwan da suke fama da wanan matsalar shi ne; su yi kokari su hade kawunansu ko dan mazon Allah ya yi alfahari da su ranar tashin alkiyama.
Zahra’u Abubakar (Dr Zara) Gama-D Jihar Kano Karamar hukumar Nassarawa:
A ganina gaskiya abin da ke kawo rarrabuwar kai musanman ga ‘yan’uwa na jini laifin iyayen ne, ko ana nuna wa karami ya raina babba ko kuma ake nuna bambanci a tsakaninsu a fifita soyayyar wani da wani a tsakaninsu ko a tsakanin dan dakin nan da dan dakin can, wannan shi ne; abubuwan dake kawo rarrabuwar juna a wasu gidajen. Laifin iyaye ne gaskiya don tun farko abun da ka gina yaro akai dashi yake tashi.
Hakan na iya haifar da matsaloli da dama saboda za ka ga kowa ba ruwansa da kowa hakan har ta kai ga iyalai suma sun shiga fadan ba ruwana da matar wane ko dan wane, kuma abun sai ka ga ya sami asali ne tun farko sanda suke gaban iyayensu.
Eh! gaskiya hanyar da ya kamata a bi a magance afkuwar hakan, hanyar ita ce; iyaye su dage tun yaransu na kanana su nuna musu kaunar junar su a rinka nuna masu ba suda fa kamar wannan dan uwan nasu su rike juna da gaskiya da amana sannan kar su rinka nuna bambanci a tsakaninsu har ta yadda yaro zai sa abun a ransa har ta kai ga girmansu ba idan kuma ‘ya’yan Kishiya da kishiya ne ki nuna musu da ‘yan nan dakin da ‘yan nan dakin dukkaninsu abu daya ne, ‘yan’uwan juna kuke har abada idan kika nuna naki ne Yaya wadancen ba ‘ya “ya bane to dole nan ma a samu rabuwar kai ko da kuwa bayan bakya ko baka duniyar ne.
Shawarar da zan basu su gyara su daidaita su kuma guje afkuwar hakan, hakan yana haifar da gaba da kiyayya me karfi a tsakanin kowa na jin haushin kowa wani ma har ya fara gushewar tunani ya ce ya cutar da dan uwansa Allah ya kyauta Allah ya daidaita tsakanin ‘yan’uwa da ‘yan’uwa.
Fauziyya S. Madaki daga Jihar Kaduna:
Wasu lokutan hakan yana samo asali ne ga yadda aka tarbiyanci yaro a kai, kamar yadda ake cewa ice tun yana danye ake lankwasa shi, haka tarbiyya da kuma nunawa yara soyayyar junansu tun kafin su girma.
Wasu kuma iyayenmu mata ke haddasa kiyayyar a tsakanin yaransu saboda kishi da sauransu. Laifin yana ga iyaye musamman iyayenmu mata yana da kyau tun yara suna kanana mu yi kokari mu koyar da su yadda za su so junansu, da yadda babba zai ji tausayin na kasansa da yadda zai dinga taimakonsa da jansa a jikinsa, kananan kuma mu koyar dasu girmama na samansu da yi musu biyayya, iyaye maza kuma su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da rashin rarrabuwar kawunan ‘ya’yansu musamman ga wanda yake da mata sama da daya.
Hakan yana iya haifar da babbar matsala a wasu lokutan, yana haifar da tsanar juna a tsakaninsu, rashin fahimta, da kuma yi wa juna hassada da bakin ciki, ya kan haifar da rashin taimakon juna, wasu lokutan ma idan Allah ya dauke ran mahaifinsu to akan rasa taimakekeniyar juna a tsakaninsu.
Kamar yadda na ce ta hanyar nunawa yara soyayyar junansu da jin kai, sannan a hada da addu’a da sanin suwaye abokanan ‘ya’yansu. Shawarata ita ce tun kafin lokaci ya kure iyaye ku koma ku gyara barakar da take tsakanin yaranku ta hanyar yi musu nasiha, da misalai da wasu da suke kwatantar taimakon junansu.
Ibarhim Danmulky daga Unguwar Gama Nasarawar Kano:
Abin da yake kawo hakan shi ne; rashin riga kafin matsalar da iyaye basa yi kafin yara su girma.
Akasari laifin na iyaye ne tunda su suke kula da yara tun kafin yara su yi wayo su gane ba dakinsu daya ba da sauransu. Rabuwar kai yana daga cikin matsalolin da hakan yake haifarwa da kuma rashin zaman lafiya a zamantakewar wannan dangi.
Maganar gaskiya magance wannan matsala abu ne mai wahala musamman idan abu ya kure yara sun gama wayo da sauransu.
Hanya mafi sauki wajen magance wannan matsalar ita ce iyaye su dage tun yara suna kanana ka da su taba nuna musu wariya da sankai, tun suna kanana a cusa musu san junansu dan ice tun yana danye ake tankwara shi.
Su kuma masu fama da matsalar nan su dage da addu’a kuma adduar ta su ta zama jama’u gaba daya akan wannan zuriyya na fatan samun hadin kai da zaman lafiya mai dorewa.