• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Kasuwa Da Cin Zarafi Na Cikin Manyan Kalubalen Kannywood – Sani Abubakar

byRabilu Sanusi Bena
2 years ago
Kasuwa

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

Wannan ita ce karshen tattaunawa da Jarumi SANI ABUBAKAR da muka fara kawowa a makon da ya gabata tare da wakiliyarmu, RABI’AT SIDI BALA. A karanta har karshe don jin abubuwan ta kunsa kamar haka:

Tun daga farkon farawarka kawo yanzu wanne irin kalubale ka fuskanta cikin masana’antar?

Shi kalubale ba a rasa shi, a gaskiyar magana tun daga farko kawo yanzu ba zan iya cewa ga wani babban kalubale dana hadu da shi ba face rashin kasuwa, yadda sana’ar ta canja ba yadda take da farko ba akalarta ta juya ta yi canji kala-kala, wannan canji da ta kawo bangaren kasuwa shi ne kawai kalubalen. Sannan babban abin da ya fi damu na shi ne za ka ga mutum ya fito ya ci zarafinmu amma ba mu da ikon ramawa su ma shuwagabanninmu sai dai kawai su zuba ido saboda gudun kar mutum ya zo yayi magana wani ya fadi maganar da hankalinka ba zai iya dauka ba, gaskiya wadannan shi ne matsalolin da nake ganin su ka fi damuna. za ka ga mutumin da bai ma san ya sana’ar taka take ba, bai ma taba zuwa ya ga ya ma ake sana’ar ba, bai san ya aka fara ta ya ake kare ta ba, amma za ka ga ya fito yana cin mutunci, ko cin zarafi yana zaginku a cikin masana’antar, kuma karshe dai abu daya kawai za a yi a ce a yi hakuri. Babu wata masana’anta ko wajen sana’a da za ka tarar ana zagin mutum ko ana cin zarafinsa kuma babu yadda zai yi sai masana’antar Kannywood. Ni dai tunda nake cikin masana’antar babu wani wanda ya taba daukar wani tallafi ya ce ga wani tallafi an ba da domin ci gaban masana’antar in dai ba maigidana ba, na tabbatar sanata ya taimaki ‘yan kannywood wanda kuma duk abin da aka yi kusan da hannuna ma a ciki, amma kalubale na cin mutunci da cin zarafi dai muna gani.

Ba ka ganin wasun cikinku ne ke nemo muku zagin, ta yadda suke tafiyar da nasu al’amuran har ta kai da an yi muku kudin goro, ko ya abun yake?

Gaskiyar magana guda daya ita ce; duk cikin al’ummar da ki ka gani, kuma kowacce irin masana’anta a duniya dole akwai bata gari a cikinta kuma akwai na kirki, dan haka babu yadda za a ce mu wankakku ne dan muna wannan maganar, a’a! dole akwai bata gari a cikinmu. Amma maganar na ce wani ne yake janyo mana zagi a’a! ai bai kamata ka yi shari’a ba tare da, ka san me ye yake faruwa ba. Dole a cikin al’umma idan kana sana’a sai ka tarar da bata gari da zai ja maka zagi wannan kuwa mun sani, hatta a cikinku ‘yan jarida ku kun sani akwai wadanda bata gari ne suke ja muku zagi akan sana’arku, ba za ku ce ku a cikin sana’arku babu mai zaginku ba, a kowacce sana’a ana zagin mutane.

Na ji ka ce ba wanda ya taba ba ka wani tallafi a masana’antar, to ya batun kallon da sauran jama’a ke yi wa ‘yan kannywood na cewar; suna tafiya ne da gwamnati, yayin da jam’iyya tayi nasara tana ware musu wasu kudade na daban, me za ka ce akan hakan?

Gaskiyar magana shi dan fim zai iya yin siyasa, misali; kamar ni kin ga tunda nake da maigidana  nake tafiya tare da shi, ni ba jam’iyya nake bi ba, bayan zaben maigidana zan duba na ga wa ya cancanta na zabe shi?, kuma ni bana bin wani dan siyasa bayan maigidana, akwai masu yin hakan amma akwai wanda ba sa canja jam’iyya a ‘yan kannywood din. Kuma dole ai dan fim yayi siyasa saboda siyasa ta kowa ce dole ka duba ka ga ya za a yi al’ummarka ta zama gyararriyar al’umma?, misali; dole ka  duba ka hanga ka gani wane ne zai taimaki al’umma, inda gudunmawar da za ka ba shi kai ma ka bada taka irin gudunmawar, ni kin ga Barau Jibril Maliya ne maigidana, dan haka dole ina bin sa dan na tabbatar da cewa inada yakini dari bisa dari yana kyautatawa al’umma.

Ya batun nasarori fa, wanne irin nasarori ka samu game da fim?

Sai dai na ce Alhamdulillahi dan ban isa ma na ce ga iyakacinsu ba, an same su da yawa burjik kuma ana kan samu, dan cikin sana’ar Allah ya rufa ma asiri ai ka gama samun nasara, an samu nasarori babu iyaka gaskiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
Nishadi

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

October 4, 2025
Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa
Nishadi

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

September 28, 2025
Next Post
Zan Bar Barcelona A Karshen Kakar Wasanni Ta Bana-Xavi

Zan Bar Barcelona A Karshen Kakar Wasanni Ta Bana-Xavi

LABARAI MASU NASABA

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version