Nijeriya ta sake tafka irin abin kunyar da ta yi a London, shekaru 12 da suka wuce, bayan da ta sake yin abin junya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, wato Olympic, inda ‘yan wasan Nijeriya 88 da suka wakilci kasar nan suka dawo ba tare da cin kyauta ko guda daya ba.
A cikin ‘yan wasa 88 da suka tafi Birnin Paris din kasar Faransa domin wakiltar Nijeriya a wasannin, babu dan wasa ko guda daya da ya yi kokarin lashe sarkar gwal, duk da kirarin da ake yi wa Nijeriya na cewa ita ce uwa maba da mama.
- Saka Ya Saka Murmushi A Fuskar Magoya Bayan Arsenal
- Sin Ta Samu Ci Gaba A Fannin Raya Jarin Fasahohin Kere-Kere Da Kaso 10.9% A Watanni 7 Na Farkon Bana
Tuni dai Ministan Wasanni, John Enoh, ya bayyana rashin kokarin a matsayin abin kunya, domin ‘yan wasan kwallon kwando na D’Tigress ne kadai suka samu nasarar lashe wasanni biyu na cikin rukuni, inda suka doke kasashen Australia da Canada, kuma ‘yan wasan sun kafa tarihin kasancewa kasar Afirka ta farko da ta samu zuwa matakin wasan kusa da na kusa da na karshe a wasannin kwallon kwandon.
Tawagar mata ta kwallon kafa ma dai tun a cikin rukuni aka yi waje da ita, sannan ‘yan wasan da suka wakilci kasar nan a wasannin kokawa da wasannin kokawa da wasan daga nauyi da wasan kwallon tabir duka an fitar da su ne da wuri daga gasar.
Sai dai daman tun daga gasar da aka buga a Birnin London shekaru 12 da suka gabata, Nijeriya ta samu nasarar lashe sarka guda uku ne kawai cikin shekaru 12, inda a shekarar 2016 a Birnin Rio na Brazil ‘yan wasan kwallon ‘yan kasa da shekara 23 suka samu tagulla, sai a birnin Tokyo na Japan ‘yar wasan kokawa Blessing Oborodudu ta samu tagulla itama, sai Ese Brume wadda ta samu tagulla itama a Japan din.
Amma akwai kasashen Afirka da suka fi Nijeriya tabuka abin arziki musamman kasar Botswana da ta lashe sarkar gwal ta gudun mita 200, wadda kuma hakan ya kasance kasar Afirka ta farko da ta taba lashe wannan kyauta, sai Kenya wadda ta lashe gwal guda hudu sai Algeriya mai guda biyu, sai kasashen Uganda da Tunisia da Afirka ta Kudu da Ethiopia da Masar da kuma Morocco duka sun samu gwal guda dai-dai.
Sai dai akwai ‘yan Nijeriya da suka lashe kyautar gwal amma sun wakilci wasu kasashen daban, ‘yan wasan sun hada da Salwer Eid Naser, da Samuel Omorodion da Yemisi Ogunleye da kuma Annette Echikunweke duka sun wakilci kasashe daban-daban kuma sun lashe sarkoki.
Amma wasu suna ganin akwai bukatar gwamnati ta dauki mataki a nan gaba ta hanyar farfado da wasanni tun daga makarantun firamare zuwa makarantun gaba da sakandire da kuma dawo da wasanni a unguwanni domin karfafawa matasa gwiwa.