Jam’iyyar SDP reshen jihar Katsina ta bayyana cewa halin kunci da ‘yan ƙasar ke ciki yana da alaƙa ta kusa da kusa da rashin shuwagabanni masu nagarta waɗanda suke kishin talakawa.
Shugaban jam’iyyar SDP a jihar Katsina Alhaji Bello Safana ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Katsina
Alhaji Bello Safana ya koka akan halin rashin tsaro da ya sanyo Katsina gaba inda ya ce kullum sai an kawo hari yanzu abin har cikin kwaryar Katsina.
Haka kuma jam’iyyar ta SDP a matakin jihar Katsina sun bayyana cewa, sun fito ne domin kwatowa al’umma haƙƙinsu da ceto talakawa daga halin da suke ciki musamman matsalar tsaro.
Tunda farko Alhaji Bello Safana ya fara ne da bada tarihin yadda wannan tafiya ta su ta faro daga wani dandali da masu rajin kawo gyara a cikin al’umma.
Ya ce wannan tafiya Alhaji Usman Bujaje ne ya assasa ta domin a ɗora wani harsashi samar da yanayin da zai bada damar samun shuwagabannin na gari da za su jagoranci al’umma da adalci anan gaba.
Shugaban jam’iyyar SDP ya ce sun yi zaɓen shugabanni sannan sun samar da ‘
‘yan takarkari a matakin gwamna wanda Ibrahim Zakari shine ɗan takarar su na gwamnan Katsina sannan suna da
‘yan takarar majalisar dokokin jiha 18 dakuma na majalisar tarayya.
Sannan a madadin ita kanta jami’yyar SDP da magoya bayan ta a fadin jihar Katsina suna jajanta wa al’umma bisa hali na rashin tsaro da aka shiga cikin sa, kuma suna fatan cewa idan aka zaɓe su za su kawo canji mai ma’ana.
Shima a nashi jawabin sakataren jam’iyar SDP na jihar Katsina Alhaji Mustapha Kurfi ya nuna halin damuwa akan yadda jama’a suka shiga halin rashin tabbas da rashin sanin makomar ƙasa baƙi ɗaya
Haka kuma shuwagabannin jam’iyyar SDP sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake da tafiyar da sha’anin tsaro a Najeriya da kuma jihar Katsina wanda suke ce ta hanyar shuwagabannin na gari ne kawai za a yi Kawo karshen wannan matsala
Daga karshe shuwagabannin jam’iyyar SDP sun bayyana cewa an shirya tsaf domin tunkarar duk wani ƙalubale na siyasa ta hanyar sanar da al’umma hali da jihar Katsina da kuma ƙasa baki ɗaya suke ciki.