Shafin Taskira shafi ne da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma ta bangarori da dama, haka kuma shafin na karbar sakonnin masu karatu game da matsalolin da suka dame su domin tattaunawa akai. A yau ma shafin na dauke da wani sakon wata baiwar Allah, wanda aka bukaci a sakaya suna, inda sakon ya fara da cewa;
“Ni mahaifiya ce mai yara biyar, Ina da ‘yan uwa mata wadanda suka yi aure, suna da yara biyu kacal. Kuma sun fi ni arzikin kudi, amma a mafi yawan lokuta ba sa son su taimake ni. Na roke su da su yafe min idan na zalunce su. Duk shekara suna kai ‘Ya’yansu kasar waje hutu, amma ba su taba cewa daya daga cikin ‘Ya’yana ya bi su ba ko da mutum daya ne. Yanzu lokaci ya yi da za a biya kudin makarantar yara kuma ba da jimawa ba kudin hayarmu zai kare. Albashin mijina ba zai iya daukar duk wadannan kudaden ba, kuma ‘yan uwana sun sani amma sai sun jira na zo na tambaye su tukunna kafin su taimake ni, kamar mabaraciya. Ku ba ni shawara kan yadda zan tafiyar da wannan lamarin”.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin, game da wannan baru; Ko abin da ‘yan uwanta suka aikata ya dace?, Idan ke ce ko kai ne ka ci karo da irin wannan matsalar wanne mataki za a dauka?. Sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Sunana Hafsat Sa’eed daga Neja Karamar Hukumar Suleja:
Gaskiya ni dai a tunanina ko tun farko ba su tashi da zumunci bane shiyasa, ko kadan bai dace ba, domin kuwa musulunci bai koyar da mu rashin imani da rashin tausayi ba, asali ma ya koyar da mu da imani da tausayi da kuma taimakon mara shi, bare kuma dan uwa karewa ma kenan. In ni ce babu matakin dabzan dauka daya wuce in dogara da Allah, in kuma dage da neman halak dina domin in taimaki kaina da ‘ya’yana, don su ma ba wayo suka yi wa Allah ya basu ba, kazalika kuwa ni ma bai manta da ni ba, kuma me nema na tare da samu. Shawarata ga masu irin wannan halin kuwa shi ne; Su ji tsoron Allah su taimaki ‘yan uwansu don babu wanda ya san goben wani, domin kuwa in ita ba ta da shi yau, babu ruwan Allah gobe ya karbe agurinsu ya dawo da shi gare ta, ko ma ‘ya’yanta Allah ya sa mu dace.
Sunana Mas’ud Sale Dokatawa:
A zahirin gaskiya hakan yana faruwa kuma wasu ‘yan uwan suna kasa fahimtar cewa Allah ne ya basu, amma sai ka ga sun zama kamar ‘ya’yan karuna, ba sa tausayawa da taimakawa ‘yan uwansu na jini da bare, wanda ba na jinin ba. Su sani cewa Allah zai iya karbewa ba tare da shawara da su ba, don haka su inga bawa ‘yan uwa su ma sai Allah ya yalwata musu. Abin da suka yi basu kyauta ba duk da ba a ji ta bakinsu ba watakila laifinta ne, ba nasu ba. In ni ne aka yi wa haka zan dauki matakin hakuri da kuma jajircewa wajen neman na kaina, sannan zan yi iya kar kokarina wajen yin maneji da abin da na samu, ba sai na nemi taimakon su ba ma. Shawarar ita ce su ji tsoron Allah su tuna da hakkin zumunta dan addini, wajibi ne ka taimaki dan uwanka matukar kana da hali, balle shakiki ma. Shawara su gaggauta tuba da kuma jawo ta a jikinsu su kyauta ta mata, hakan zai fi.
Sunana Fatima Kano daga Jihar Kano Unguwar Gwammaja:
Da gaske wannan ‘yan uwa ba su kyautata ba, ‘Yar uwa ciki daya ai ya fi karfin wasa, kamata yayi su taimaka mata tunda ba su da yara da yawa, ko da ace ba su santa ba idan ka taimaki wani kai ma Allah zai taimake ka.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) daga Jihar Kano Rano LGA:
Ai ni yanzu ban ga abin da zan ce ba duba da ita kanta bata fadi dalili ko hujjar da suke yi mata hakan ba, kawai dai ta kawo abin da yake damunta a karan kanta dana yaranta, sai na ce Allah ya daidai ta su, idan kuma ta san akwai abin da ta san ya taba hada su ta je ta nemi yafiyarsu koda ita ce sama da su. A’a maganar gaskiya idan muka yi koyi da halayen ma’aiki (s.a.w) bai dace su yi mata haka ba koda ace tayi musu wani laifin sabida yana da kyau koda waninka ya yi ma abin sharri kai kuma ka mayar masa da alkairi, wanda hakan ma zai iya canja shi shi ma ya zama na kirki din. Hakuri da addu’a sannan a ci gaba da neman na kai, sannan idan na san ni ne mai laifi a dangane da halin da nake ciki da ‘yan uwana sai na neme su na basu hakuri, haka idan sune zan dinga basu shawara ko na dinga hada su da wanda suke jin maganarsa, domin mu zamo tsintsiya daya madaurinki daya. Shawara ta anan ita ce; mu yi koyi da halayen fiyayyen halitta ka da mu zama masu aikata abin da mu kanmu mun san ba daidai bane, muna jan ‘yan uwanmu jikinmu idan mun sami damar hakan.
Sunana Abba Ibraheem Isma’el daga Jihar Kano:
A gaskiya ba su kyauta ba ko da ace a baya kin sami dama ke ma kin wulakanta su, barinta ne ina tunanin ba haka bane, tunda Manzo Allah ya ce duk wanda ya mu’amalance ka da halin banza to addini ya bada dama ka ramar amma kuma hakuri ya fi alkhairi, barinta ne ba wani laifi da tayi musu kuma su kasa kyautata mata kuma su tuna Allah ne ya wadata su ba wayansu ba, ita ma Allah zai iya tsiyatar da su kuma ya wadata ta, su zo neman taimako gurinta, ina rokon Allah ya ganar da masu irin wannan dabi’a. A ce ni ne a cikin wanan halin zan dauka kaddara ce daga Allah kuma bawa baya wuce wa kaddararsa, amma idan ta yi hakuri komai mai wuce wa ne.
Sunana Hassana Hussain Malami (Haseenan Masoya) daga Jihar Kano Gwarzo LGA:
Gaskiya wannan al’amari da ‘yan uwanta suke nuna mata sai dai idan akwai matsala tun farko, matsalar kuwa ita ce sai dai ta samo mafari ne tun daga wajen iyayensu, sabida mafi akasari iyayenmu yanzu wasu suna nuna bambanci tsakanin ‘ya’yansu sai ki ga uwa ta ware daya daga cikin ‘ya’yanta tana fifitawa toh! su kuma ‘yan uwan nasu abun ne yake bakanta musu rai shiyasa suka kullace ta. Tom ni dai in da ni ce a wanna mataki zan tambaye su me nayi musu?, kuma zan basu hakuri idan kuma basu gyara ba, tom zan hakura da taimakonsu na nema a taskar Allah, amma kuma hakan ba zai sa zumuncinmu ya lalace ba. Tom gaskiya abun da suka yi bai dace ba, ai ko me dan uwanka zai yi hannunka baya taba rubewa ka yanke ka yar sai suyi hakuri. Ni dai sai dai nace Allah ya ganar da su gaskiya, domin Allah sai ya tambaye su, sabida idan Allah ya baka arziki tom yana nufin ya nada ka wakilci a dangi.
Sunana Ibrahim Surajo:
Maganar gaskiya Idan Allah ya ba wasu mutane arziki a cikin zuri’a to fa ya ba su ne domin su taimaka wa ahalinsu da sauran mutane, ba wai na su bane su kadai. Gaskiya wadannan ’yan uwan nata ba su kyauta ba, tunda sun san halin da ‘yar uwarsu ta ke ciki ya kamata sai ta roke su ba, kafin su taimaka mata. Mu ma kuma fa bai kamata mu rinka yin shiru muna tunanin ‘yan uwanmu masu hannu da shuni sun san matsalolin mu ba tare da mun sanar da su ba, domin a wasu lokutan fa za ka rinka gani kamar ‘yan uwanmu masu hali suna sane da halin da mu ke ciki, bayan kuma ba haka bane, kuma Idan muka fada musu suna share mana hawaye. Su kuma masu irin wannan halin ya kamata su janyo ‘yan uwansu a jiki, su rinka bibiyar halin da suke ciki, hakan zai ba su damar sanin damuwar su har ma su taimaka musu.
Sunana Mustapha Abdullah Abubakar daga Filato Jihar Jos:
Shawara ta anan ita ce ki samu abun yi domin dogaro da kanki, hakan na tabbata zai taimake ki kuma ya taimaki mijinki, duba da yanayin halin na rashin wadata da ku ke fama da shi. Gaskiya abun da suka yi mata bai dace ba kwata-kwata, amma yanzu wannan zamanin da muke ciki ‘yan uwanka idan baka tambaye su ba, ba sa ma tunanin wanne irin mawuyacin hali ka ke ciki ba. Gaskiya idan ni ne matakin da zan dauka shi ne; idan ina da hali zan yi iya kokarina wajan taimaka mata da ma masu irin wannan matsalar irin nata. Shawara ta ga masu irin wannan dabi’a shi ne; su ji tsoron Allah subhanahu wata’ala, sannan su tuna cewa a kowane yanayi rayuwa tana iya juyawa wataran za su bar ma duniya ma’ana za su mutu su tafi su bar ‘ya’yansu, har ta kai a rasa masu taimakonsu su ma, yanzu ne suke da damar taimakon ‘yan uwansu mabukata.
Sunana Sadiya Garba Umar Jihar Kano:
To da farko dai tayi hakuri ta ci gaba da kau da kanta a kansu da abin hannunsu ta sawa ranta suma ba su da shi, ta tashi ta nema a wajen Allah ta kama sana’a Allah zai duba kyakkyawar zuciyarta ya sa mata nasibi a cikin kasuwancinta yadda za ta dauki dawainiyar ‘ya’yanta. Su kuma ba su kyauta ba, ba su san alkhairi kamar taki bane a cikin arzikin da Allah ya yi maka, wallahi duk me badawa sai Allah ya kara masa idan ka fitar da kadan sai ya baka me yawa, ai ba sai ma ta zo ta tambaye su ba tunda sun sani tana da karamin karfi a cikinsu ya dace su cire mata damuwar rashi tunda suma ba rawa suka yi wa Allah ya basu ba, kuma ba wai dan ya fi son su ba, a’a kawai shi ubangiji me hikima ne ba mamaki itan idan ya bata su zame mata matsala gwara zamanta a hakan. Idan ni ce gaskiya zan dauke kaina a kansu saboda ni ban ma yarda da abin wani ba na fi ganewa ko za ka ba ni ni ma ina da nawa. Kuma idan har mutum ya samu ‘yan uwa irin haka to ina me bashi shawarar ya dauke idonsa daga kansu koda duk juma’a a saudiyya suke sallar juma’a, karewar arziki kawai ka tsaya ka nemi naka shi ne. Shawara ta anan shi ne mu tashi mu nemi na kanmu zaman banza, rashin abin yi, shi ke sa ka zauna ma tunanin wane yana da shi, idan har kana da abin yi wallahi baka ta tashi bare ma abin da ya ke da shi.
Sunana Sani Haruna daga Jihar Kano:
Abu na farko dai za a kira wannan da rashin Imani, sabida duk wanda ba shi da halayya ta taimakon mabukaci ba to tabbas bai yi imani da umarnin shugaban halitta ba, Annabi Muhammadu (s.a.w). Maganar abin da ‘yan uwanta suka yi sam babu dacewa ga mumini ko da kafiri ne, balle wanda ya yadda da Allah ya shaida da zuwan Manzan Allah (s.a.w). Tabbas Idan ni ne na ci karo da wannan matsalar ina da mafita anan, sabida Allah ya gama yi min arziki tunda ya bani lafiya, Miji, ‘Ya’ya har biyar, ka ga kuwa Allah bai so na wulakanta ba, hausawa suka ce babu maraya sai rago, tabbas! haka ne, Idan ka zauna za ka ga zama, Idan ka jira wajen wani za ka ga wulakanci kala-kala, Za mu mike mu roka wajen Allah, kuma mu mike tsaye da sana’a duk kankantar ta to anan Allah zai yi ikonsa ga wanda ya yi niyar taimakon kansa, hakan ma sunna ce ta Annabi Muhammadu (s.a.w). Shawara ai gani ga wane ya ishi wane tsoran Allah, su masu irin wannan dabi’a su tuna da an yi wasu kafin su, babu wajen zaman kudi ko amfanin kudi a makomar musulmi ko kafiri, kuma da duniya ake gina lahira, ita ma mai jira wajen ‘yan uwan ta wannan karatu ne daya ishi ‘yan baya masu dabi’a irin ta ta, Allah ya sa mu dace dan shugaba (s.a.w).
Sunana Abdul M. Sufyan daga Zariya:
A gaskiya hakan da suka yi mata ba su kyauta ba, kuma in ni ne ba zan gajiya ba wajan zuwa gare su, domin ina da tabbacin hakurin da nake yi da su zai yi min rana. Haka zalika a mafiya yawan lokuta ba kasafai masu kudi suke wadatuwa da tunanin taimakon ‘yan uwansu ba, sun fi son mutum ya bukaci taimakonsu fiye da ya jira zuwan kansu gare shi. A karshe ina fatan duk masu kudin dake irin wannan hali Allah ya ganar da su, su gane zumunci fadar Allah ne.
Sunana Fatima Gwammaja (Super):
Ba bukatar ka roki mutun bayan ya san kana da bukatar taimakonsa, hakan zai kawo maka wulakanci, da ma basu san halin da ki ke ciki ba sai ki nemi taimakonsu amma sun sani, Idan akwai wani abu kuma da ki kai musu wanda suka rike ki a ransu sai ki nemi gafararsu, su yafe miki saboda babu wanda ya kamata ya tausaya maka da yafi dan uwanka.
Sunana Muhammad Nasir daga Jigawa Dutse:
Abin da zance a gaskiya ba su kyauta ba, abin da suka aikata kwata-kwata bai dace ba. Idan ni ne zan yi juriya da hakuri akan halin da Allah ya jarrabce ni da shi, zan fawwalawa Allah komai, domin shi Allah (S.a.w) baya yin kuskure. Masu wannan dabi’a ya kamata su sani cewa su ma ba wayonsu bane ya ba su Allah ne ya ba su, kuma idan ya so zai iya karbewa a koda yaushe. Sannan su sani cewa Allah ba ya basu wannan dukiya bane don kawai su ji dadi su kadai ba, dole akwai hakkin ‘yan uwa da Allah ta’ala ya wajabta musu da su taimake su, domin arzikin ba nasu bane su kadai, akwai hakkin ‘yan uwa na jini da kuma masu karamin karfi.
Sunana GM Hoody Booth:
Babu dacewa ga zuwa neman taimako ta hanyar roko wajen ‘yan uwanki dan sun fi ki arziki, amma ba laifi bane yin hakan ta hanyar bin da ta dace, a cikin yaranki biyu a samu wanda zai je sanar da su komai amma sai an daure da fuskantar kowanne irin abu.
Sunana Kabir A Ahmed daga Jihar Kano Unguwar Dabai:
Gaskiya ‘yan uwanta basu kyauta ba ni shawarata shi ne; Ta mikawa Allah al’amuranta Allah zai kawo mata mafita.