Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Sarkin Moroko Mohammed VI bayan mummunar girgizar kasa da ta afku a kasar a ranar Asabar, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Shugaban ya jajantawa dukkan iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da duk wadanda bala’in ya shafa, tare da fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa.
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya tabbatar wa gwamnatin da al’ummar kasar Maroko cewa, addu’o’i da zuciyotin ‘yan Nijeriya na tare da su a wannan mawuyacin lokaci na jarrabawa da alhini da kasar ke ciki.
Talla