Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar, sakamakon yawaitar hare-hare da kashe-kashen da ake yi a birnin.
A cewar gwamnan, an takaita zirga-zirgar babura da masu tuka keke napep a tsakanin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja
- Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano
Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati, ranar Talata.
Ya ce, amma dokar ta kebe cibiyoyi da hukumomin kiwon lafiya.
Ya bayyana cewa, sabon matakin na da nufin dakile matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa a babban birnin jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnati ba za ta rungume hannu ba, yayin da masu aikata laifuka ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Ya kuma umurci gundumomi, ƙauye, da masu unguwanni da su sanya ido kan duk wadanda ke zaune a yankunan su.
Ya kuma yi gargadin cewa, duk gidan da aka samu yana dauke da masu aikata laifuka ko masu safarar miyagun kwayoyi za a ruguza shi.
A baya-bayan nan dai garin Minna ya sake samun koma-baya na ‘yan daba, da hare-hare, da kashe-kashe, lamarin da ke janyo firgici da damuwa a tsakanin mazauna garin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp