Majalisar wakilai ta yi kira ga shugabannin tsaro da su kaddamar da wani shiri na tsaro na rundunar hadin gwiwa ta musamman a kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya da ke Jihar Neja domin fatattakar ‘yan bindigar da suka addabi yankin.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Ismail Modibo (APC-Neja) ya gabatar a zauren majalisar a Abuja ranar Laraba.
- An Gudanar Da Bikin Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Serbia A Belgrade
- Gwamna Nasir Ya Bada Gudunmuwar Naira Miliyan 100 Ga Kungiyar Lauyoyi Kan Gina Sakatariya A Kebbi
Da yake gabatar da kudirin, Modibo ya ce, mazabar Shiroro, Rafi, da Munya ta tarayya na fuskantar ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga.
Ya bayyana cewa yankin ya na fama da hare-haren ‘yan ta’adda da suka hada da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu a ‘yan kwanakin nan.