• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

by Idris Aliyu Daudawa
1 month ago
Tsaro

Azuzuwan makarantu a Jihohin Benuwe, Katsina da kuma Neja yanzu an maida su wuraren kwana na muatne ƴan gudun Hijira waɗanda aka raba su da gidajensu sanadiyar ayyukan ta’addancin da ƴan ta’adda suke yi. Dubban yaran da suke waɗanɗan Jihohin yanzu basu zuwa makarantu saboda kuwa makarantun nasu an maida su, matsugunnin mutane ƴan gudun hijira.

Halin da ake ciki kuma yanzu basu san ranar da za su koma makaranta ba, irin hakan ta sa ake ganin ko shakka babu lamarin karatu zai haɗu matsala a wuraren kamar yadda rahotannin jaridar, Trust ta ƙarshen suka nuna.

A Jihar Benuwe, babu wanda zai iya faɗar yadda za’a yi da irin yadda yaran da suka isa shiga makaranta, waɗanda matsalar ƴan ta’adda ta lalata wurarensu, waɗanda kuma mutanen ne suka mamaye makaratun domin su samarwa kansu wuraren da za su riƙa kwana.

  • Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar
  • SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

Rahotanni sun nuna muatane da yawa daga rikicin ta’addanci ya fi shafar ƙananan hukumomi sun haɗa da Guma, Logo, Agatu, Kwande, Gwer ta Yamma, Apa da kuma Makurdi, yanzu al’ummar ƙananan hukumomin suna kwana ne a makarantu, hakan kuma ya kawo tsayawar harkokin da suka shafi karatu.

Wata mahaifiya, Anita Ikyur, ta ce makaranta Firamare ta NKST, a ƙaramar hukumar Logo da daɗewa ne ta zama mazauni shekarar biyar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma.

“Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu.

“Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin itatuwa, yayin da wasu kum asuka daina zuwa makaranta gaba ɗaya kamar yadda Achagh ya ce”.

Ga Jacintha Terhemen, wadda ita ɗalibi ce ‘yar makarantar Sakandare a wani harin ta’addanci da aka kai a Yelwata, ƙarƙashin ƙaramar hukumar Guma, cewa tayi duk da yake, makarantar da take abin bai shafe ta,ba saboda babu mutanen da suke kwana, amma, a, makarantun Firamare ana amfani ne, da su tare da mutanen da ta’addancin ƴan ta’adda ya raba su da garuruwan su.

“A sansanonin Ugba a Logo da Ortese a Guma, ana zuwa makaranta yayin da suma ƴan gudun Hijirar suna nan. Gwamnatin Jihar Benuwe ta ƙaddamar da wani tsari na samar da wuraren kwana masu inganci, amma hanya da za abi ita ce take da wahala sai an sa haƙuri.

An riga an sa tsari, gwamnati kuma tana neman taimako daga majalisar ɗinkin duniya da kuma Tarayyar Turai da sauran abokan tafiya masu taimakawa daga waje domin a aiwatar da shi tsarin. Aikin ana sa ran zai ci Naira Tiriliyan ɗaya, don haka abin yana buƙatar kuɗi da yawa ya kuma ƙunshi dukkan abubuwan more rayuwa waɗanda daga ƙarshe za su kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta.

Neja

Makarantun da ake amfani da su a Jihar Neja wajen matsugunnin ƴan gudun Hijira sun haɗa da Central Firmare, Gwada; Central Firamare School, Kuta and Central Firamare, Erena, dukkansu a ƙaramar hukumar Shiroro.

Ɗaya daga mutanen da suka rasa matsuguni, Ahmed Almustapha, da yake sansanin Kuta, ya shaidawa Jaridar ƙarshen mako cewa wasu daga cikin yaran an maida su zuwa Model Firamare yayin da ƴan azuzuwa ne aka bar ma, sha’anin da ya shafi karatu a Central Firamare.

“Ba duka azuzuwa bane, ƴan gudun hijirar suke amfani da su ba. Wasu azuzuwan har yanzu ana amfani da su ne wajen yin karatun yara a makaranta, amma wasu Iyaye sun cire ‘ya’ansu daga Central Firamare,wurin da, ƴan gudun hijira suke zama, suka sasu a makarantar Model, Firamare.’Ya’yan mutanen da ta’addanci ya rutsa da sune kawai basu zuwa makaranta yanzu.

Wasu malaman da suke koyarwa ƴan sa kai su kan zo su koyar da su, amma yanzu sun bar zuwa.Bamu san dalilin da yasa ba,”.

Da yake makarantun da abin ya shfa ƴan gudun Hijira ne suke kwana, yawancin ƴan makarantar, an tilasta masu ne su koma wata makarantar, ko gaba ɗaya ma su bar zuwan. Wannan halin ba wai lamarin karatu kaɗai ya shafa ba,ƴan makaranta da Malamai, har ma ya maida wasu abubuwan da ake amfani, da su, sun lalace, hakan yasa cikin makarantar bai da wata sha’awar kallo . Shugaban makarantar Central Firamare, Kuta, Ya’u Ibrahim ya ce an bar shi da azuzuwa 9 kaɗai bayan kuma ga yawan ƴan makaranta da ya kai 1,360, inda yace sauran azuzuwan ƴan gudun hijira ne suke zama.

Tsaro

Ibrahim ya nuna rashin jin daɗinsa akan irin halayen su ƴan gudub hijirar, musamman ma yadda suke yin kashi a fili wanda yin hakan ba ƙaramar matsalar da take shafar lafiya bace, ga su Malamai, da kuma ƴan makaranta.

“Maganar gaskiya kasancewar ’yan gudun hijira ba ƙaramar matsala bace ga lamarin daya shafi lafiya gare mu. Suna kashi duk inda suka ga dama cikin makaranta, yanzu ko ina wari yaje yi.

“Yaran da su ma basu da matsuguni ba a sa su, makaranta ta, ba; ban san ko wane dalili bane ya sa. Babu waniɗan makarantarmu da ya bari saboda akwai ƴan gudun hijira a makarantarmu. Babbar matsalar da muke fuskanta ita ce rashin isassun azuzuwa saboda sai da muka raba ƴan makarantar uku, wato kowace rana da akwai waɗanda za su zo saboda yawansu ana kuma son a kauce ma cunkoso. Ga kuma irin yadda ake zama a sansanin wani abin damuwa ne shi ma kamar yadda ya ƙara jaddadawa”.

Katsina

An lura da cewa a Jihar Katsina da akwai yara waɗanda basu zuwa makaranta su kuma ne ke ta gararanba kan titunan manyan garuruwa a faɗin Jihar saboda lamarin da ya shafi ta’addanci da sauran laifuka. Da yake basu da wani wuri takamimi da aka ware masu domin su zauna a duk faɗin Jihar, yawanci suna zama ne da danginsu waɗanda suke a manyan garuruwa,ya yin da wasu suke zuwa makarantu ko wasu gine- gine ma mutane,irin hakan ko shakka babu yna shafar ilkimin yara a wasu makarantu.

Bada daɗewa bane mutanen da suka rasa matsugunin su daga wurare 12 daga ƙananan hukumomin Bakorı da Faskari waɗanda aka tilasta ma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Next Post
Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

Ban Taɓa Nadamar Shiga Fim Ba – Kabiru Nakwango

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Tsaro

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.