Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da halin wasu mazajen na rashin yaba kwalliyar matansu.
Har yanzu dai muna kan wannan batu inda a wancen makon muka ji ta bakin Binta Umar Abbale game da wannan matsalar da take ci wa Mata tuwo a kwarya na rashin yaba kwalliyarsu.
Da farko, ni dai mai wannan shafi a nawa tunanin da kuma fahimtar; wannan matsala na faruwa ne ga wasu mazan, domin ba dukka ne aka taru aka zama daya ba, akwai masu yabawar kamar yadda akwai masu rashin yabawar.
Duk da cewa mafi akasarin masu nuna halin ko in kula ga matansu ta wannan bangare wato rashin yaba kwalliya, sun fi rinjaye fiye da wadanda suke yaba kwalliyar matansu.
Duk da cewa cikin Mazan da mata ke kallon ba sa yabawar suma cikinsu akwai masu yabawar sai dai rashin ganewar da su matan ba sa yi, domin wasu Mazan ba furtawa suke kai tsaye ba, sukan isar da sako ne ta hanyoyi daban-daban, ya yin da wasu kuma suke furtawa a zahirance har kunnuwa su ji.
Hakika wannan matsala ce babba wadda da yawan wasu mazan su ke kallonta a matsayin karama na rashin yaba kwalliyar matansu, ya yin da suka yi Kwalliya da Ado dominsu.
Mafi yawan mata na bata lokutansu wajen ganin sun gyarawa mazajensu kansu ta yadda zai kallesu tamkar ba su ba cikin armashi da birgewa, sukan kashe kudade masu yawan gaske don siyan kayan kwalliya irin na zamani tare da abubuwan jan hankali na Ado ga mazajensu, Sai dai kuma mafi yawan akasarin maza basa nuna halin ko in kula ga su matan nasu yin hakan, musamman lokutan da suka tsara adon da kawalliya dominsu.
Mafi yawan Mazan na kallan Matan su wuce ba tare da nuna wata alama ta yabawa ba. Kamar yadda na fada a baya wasu mazan na isar da sakon yabo ga matan nasu ya yin da suka yi kwalliya ba tare da matan sun fahimci yabo ne ba.
Misali; Wani Namijin ya kan kalli matarsa ya yin da ta yi kwalliya har ta birge shi ya sakar mata da lallausar murmushi me ratsa zuciya wanda ita kanta ta san iya kallon da ya yi mata kadai da kuma murmushin da ya sakar ma ta ya isa ya ba ta amsar cewa kwalliyarta tayi, sai dai wata ta kan rasa gane cewar wannan sakon da aka aiko domin wannan kwalliyar ne ko da kuwa bai furta cewa ta yi kyau ba.
Wani namijin ya yin da ya ga mace ta yi kwalliya kuma ta yi kyau ya kan bukace ta nan take ba tare da ya shirya yin hakan ba, ya yin da ita kuma takan rasa gane musabbabin afkuwar hakan sai me nazarin gaske za ta iya gane wa, tun da ba furta ma ta ya yi ba.
Wani namijin da ya ga matarsa tayi kwalliya ta birge shi ya kan shirya fita unguwa ta musamman ba tare da sanin dalilin fitar ba, yayin da ita kuma takan bata rai kan ba ta shirya fita a lokacin ba, sai me nazarin gaske za ta iya gane kwalliyarta ce ta janyo hakan. Wani namijin idan ya ga matarsa ta yi kwalliya ta birgeshi musamman ya ga za ta fita zai yi gaggawar dakatar da ita ya ce ta tsaya shi zai kaita, ya yin da ita kuma take kallon hakan a matsayin rashin yarda ne ya janyo hakan, sai me nazarin gaske ce za ta gane kwalliyarta ya ja hakan.
Wani kuma idan ya ga matarsa na kwalliya ta na birge shi ya kan yi mata alheri ba tare da ta san dalilin yin wannan alherin ba tun da bai furta mata ba, sai me nazarin gaske.
Wani namijin kuma idan matarsa na kwalliya yana kalla ya na jin dadi ko da bai furta ma ta ba ya kan siyo abubuwan kwalliya ko na Ado ya kawo mata kyautarsu ba tare da ta fahimci dalilin yin hakan ba, sai me nazarin gaske.
Wani kuma da zarar ya ga matarsa ta yi kwalliya ta birgeshi ya kan fada ma ta kai tsaye cewar ta yi kyau sosai tare da hadin wasu kalamai na musamman masu isar da sakon, da kwantar da zuciya cikin soyayya. Wani kuma ya kan iya hada wa gaba daya abubuwan dana lissafo har da wanda ban lissafo ba, kowa da irin nasa salon.
Idan muka koma ga marasa yabawa kuma za mu ga cewar wasu mazan suna kin fadar hakan ne sabida; Rashin sabo na fadar, tun a farkon aure ba a saba fada ba.
Wasu kuma ganin matan ba sa yaba ta su kwalliyar yasa su ma ba sa yabawa matan, dan wata ba za ta taba ganin mijinta ya yi shiga tsaf! ta ce masa ya yi kyau ba ko da kuwa bai yi kyau din ba, ta fi bukatar ita ta yi ya yaba, amma shi in zai shiga dari fita dari ba za ta yaba nasa kwalliyar sa ba, duk da cewa wasu matan na yabawa mazan ko dan su koya su rinka yaba musu amma sai mazan su yi biris su ki yabawa matan. Wasu kuma auren ne da aka yi babu so ko kankani aure ne da aka yi shi tamkar na sadaka babu kaunar juna balle fahimtar junan.
Wasu mazan kuma na kallon mace ne da zarar an kwan biyu da aure shikenan duk wani so, kauna, kulawa, yabawa, tarairaya, tausayi, kalamai da sauransu sun kare kanta sai dai a koma furta wa na waje, wannan yasa ba sa iya furta kalmar yabo gare ta, ko da sun yi niyyar furtawar sai su ji wani iri, su fasa. Wasu kuma ganin matan tun daman can ba sa kwalliyar tun wadda aka yi farkon aure sai aka daina sai bayan da aka auro wata sannan mace za ta fara nemo hanyoyin tsafta da kwalliya da Ado ta yi, kuma ta ce ya yaba.
Wasu mazan kuma akwai tsarin kwalliyar da suke so su ga mace ta yi, amma matan ba su sani ba, mace me nazari ce kawai take iya ganewa da kuma mazan da suka san salon zance da iya sarrafa harshe na isar da sakon gyara ne kadai ke iya isar da sako ba tare da ran mace ya baci ba. Wasu kuma rashin sanin sirrin zaman aure ne da kuma jin dadin zaman auren ke haifar da hakan.
Rashin yabawar na haddasa matsaloli da dama tare da damuwa cikin zuciyar mata har ta kan iya haifar musu da ramar da ba a san dalilin afkuwarta ba ko da kuwa akwai ci da sha, domin mace za ta zamo me yawan zargin mijinta na mu’amula da wasu matan banzan na waje, zuciya ba ta da kashi.
Mace ‘yar kwalliya ce kamar yadda kowa ya sani, kuma zamani ya kara canja hakan sabanin yadda zamanin baya ya shude, idan aka yi wa mace aure a baya ita da kwalliya ta kare duk da cewa wasu ne suke maida kansu hakan ko da a zamanin bayan ne, amma a yanzu kai ya waye na cewar mace ba ta tsufa gidan mijinta.
A yanzu mace na iya kashe kudadenta dan ganin ta gyara wa miji kanta ko da kuwa ba dan gudun kishiya ba, za ta gyara jikinta ko dan jin dadin jikinta da kuma gudun lalacewa, da farantawa maigida da gudun hange-hangen wasu matan na waje da dai sauransu.
Sai dai wasu daga cikin mazan ba sa kulawa da matansu na ganin sun yaba kwalliyar da suka yi musu, ya yin da gefe gudu kuma suke can suke yabawa matar da ta kusa haifarsu wata ma ta haife su, ko matan banza ai ta zaga kafafen sada zumunta (Social Media) da gidajen kallo kala-kala ana kallon mata ana yaba kwalliyarsu.
Wasu kuma suna jin kansu ne girman kai da fadin rai, izzah, da isa, shi yake hanasu su furtawa matansu kalmar yabo ko kankani, ji suke muddin suka yabawa mace kwalliya toh girmansu ya zube gaba daya, raini ne zai biyo baya a nasu ganin. Wannan a takaice kenan.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa; inda suka fayyace dalilin da ke haifar da hakan, da abin da ke janyo hakan, da hanya da Mata da Mazan za su bi domin magance wannan matsalar, tare da shawarwari. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) Jihar Kano 08088615600:
Anan sai na ce duk macen da ta ruski kanta da samun irin wannan miji to tayi hakuri kar ta gaza ko ta ce ni ba zan ba in ma na yi ba yabawa yake ba, ki ci gaba da yi har Allah ya sa wata rana ya yaba miki. Gaskiya yana da kushe dukan karsashin mace wajen son yin ado da awaliya, sai ki ga mace ta koma wa ta daban ko kuma ya zamana in kin ganta da kwaliya a fuskarta to biki za ta je ko suna. Masu irin wannan halin su sauke girman kai a rinka yaba wa mataye in sun daddage wajen caccada kwaliya, karin armashi ma a rinka ba da dan hasafin in tayi maka kwaliyar atom, Allah yasa su gyara.
Zahra Abubakar (Dr Zara) daga Jihar Kano, Karamar hukumar Nassarawa Gama-D:
Matan da suke yi wa mazajen su kwalliya amma mazajen ba sa yabawa gaskiya abun babu dadi, amma ya kamata ita matar kar ta fasa ta ma kara dagewa ta ci gaba da kwalliya kala-kala ko ba komai ita ma za ta ji dadin jikinta in tayi kwalliya ta tsabtace ko ina kuma za ki fi samun ‘fresh air’ da kuma lada me dumbun yawa. Gaskiya dalilin shi ne rashin nuna kulawa ne daga shi mijin ka dawo ka tarar da matar ka ta ci kwalliya ta gyara ko Ina ai ta can-can-ci a yaba ma ta a gode ma ta ai ma ta kalamai masu dadi hakan ne zai sa taka cewar ba fa a banza take yi ba wanda take yi dominsa ya san tana yi sai ta kara samun dama ta dage dari bisa dari.
To hakan gaskiya zai iya haifar da matsala babba da kuma kunci da bakin ciki da damuwa saboda dole za ta ji babu dadi kuma idan ba ta kai zuciyar ta nesa ba, ko kuma me wayo ce da dabara ba wallahi wa ta watsar wa za tai ko ta gyara ko ina ba za tayi kwalliya ba saboda ta san in tayi ma babu yabo babu fallasa daga nan kuma sai a fara ai matar wane ba ta kwalliya bayan kuma kai ne sanadiyyar rushewar dainawar ta ta ko kuma ka ji ana cewa ba ta kwalliya sai za ta fita. Eh to hanyar da nake ganin hanyoyi ne da Mata za su bi domin gyara wannan matsalar ita ce idan sun yi kwalliyar in ya dawo ya huta ki ga ya gama uzurin sa bai yabi kwalliyar ki ba sai ki nuna masa, kamar misali Abban wane, ko kuma wasu kalaman dai wanda ki ka zaba masa nayi kwalliya domin ka amma ba ka ce komai ba, ba ka bawa kwalliyar nan maki ba ko dai in je in sake wata ne? a haka- a haka za ki rinka nuna masa har ya waye da hakan.
Shawarar da zan bawa Maza marrasa yaba kwalliyar matan su shi ne gaskiya hakan bai dace ba kuma ba dai-dai bane, saboda duk wacce yau Allah ya hadaku zaman takewa irin ta aure ka auro ta ka kawo ta gidanka to kwa yau in ta yi kwalliya wa gareta da ya cancanta ya yaba ma ta bayan ka Babu ba ta da shi duk duniyar nan kuwa da za su taru su yaba kwlliyar ta shir me ne saboda kai take tare da kai, kai ta yi dominka kuma babu wanda ya cancanta ya yaba irinka, idan ka yaba ko da ba tayi kyau ba fa ‘fine’ kwalliya ta biya kudin sabulu ‘but’ in kai ba ka yaba ba sauran al’umma suka ya ba shirme kenan an bar baya da kura. So dan Allah dan Annabi Maza a rinka yaba wa Matar ka kwalliyar ta.
Aisha Muhammad Salis:
Magana ta gaskiya wannan matsalar tana daya daga cikin matsalolin dake raunana zamantakewar ma’aurata, mace sai ta cancada kwalliya don ta birge mijinta, ta dau tsawon minti talatin zuwa awa daya tana gyara fuskarta da jikinta sai miji ya dawo gida ya gama hidimarsa bai tanka mata ba, ya za ta ji a ranta?, ta ya za ta dinga kokarin ci gaba da kwalliya bayan wanda ake yi dominsa baya yabawa?.
A nawa tunanin wannan yana daya daga cikin hali irin na mazan mu musamman na hausawa, wasu mazan gani suke raini ne su dinga yabawa matansu, wasu kuwa ba ma sa maida hankali kan matan ne balle har su fahimci canjin dake tattare da ita. Wasu kuwa rashin so ne wanda yake jawo rashin kula da dakushe abin da suka gani a tattare da ita. Magana ta gaskiya rashin yaba kwalliyar mace yana jawo ta tsinci kanta a yanayin da za ta ji ba ta san gyara kanta balle har ta zauna bata lokacin yin kwalliya, tun tana yi ba a yabawa har ta zo lokacin da ba ta san yi wanda a karshe zai iya maida ta kazama. To ni dai a nawa ganin in har kika ga mijinki baya yaba kwalliyarki, kar ki gaji da yi, sai dai duk randa ki ka yi kwalliya yana shigowa kika ga ya fara abubuwansa ba tare da ya yaba miki ba kiyi magana cikin dabara da salin magana ki sanar da shi bai ce kinyi kyau ba?
Yi kokari ki sanar da shi ta hakan ne muke fatan zai canza. Maza ma’auta ni dai shawarata anan ita ce ku yi kokarin bawa matanku kulawa wacce za ta baku damar fahimtar canjin da ke tattare da su, in matarka tayi kwalliya ka yaba mata, in tayi abinci mai dadi ka yaba mata wadannan abubuwan da kuke gani a matsayin kananan abu ba karamin girma gare su ba a zuciyar mace, sannan yana daga cikin kyautatawar zaman takewar ma’aurata.
Fatima Sunusi Rabiu Ummu Affan Marubuciya daga Jihar Kaduna.
Gaskiya hakan babu dadi, amma kar ki sare ki ci gaba da yi idan yau bai yaba ba watarana za ya yaba in sha Allahu. Har da rashin wayewa da kuma girman kai na wasu mazan musamman mazan hausawa, Su duk kwalliyar da mace za ta yi dai-daiku ne masu yabawar da kuwa wataran za ta ki yi ko kuma ba me kwalliyar ba ce sun iya kusheta da cewa ta zama wani iri, idan kuma me yi ce wasu ma idan ba ki ci sa’a ba dariya za su yi miki ko su ce kin yi kwalliya kamar wata yarinya. Gaskiya zai iya haifar da matsaloli masu yawa, kai ba ka yaba ba idan wani ya yaba ta sai ta ji a ranta to wai shi mijinta me yasa bai yabawa? Gaskiya mazaje masu haka ku gyara kafin wata matsalar ta faru. Farko dai su sauke rawanin tsiyar dake ransu, ka ja matarka jiki dan ita ce sirrinka idan tayi kwalliya ka yaba mata za ta ji ta tamkar wata sarauniya, duk wani abu da tayi domin kai ka yaba hakan zai kara mata kwarin guiwar yi sosai domin farin cikinka. Maza masu irin wannan dabi’a ku daina domin kuna jefa matayenku cikin tunani da zullimi, hakan ke sawa har mace ta sare, kai kuma ko a jikinka, haba dan Allah! Kai ya kamata ma ka sayo mata kayan kwalliyar, wallahi idan kana yabawa ita da kanta kan ka saya ma za ta saya da kanta. Masu irin wannan hali Allah ya sa su gyara 08104335144.
Auwalu Abdullahi Umar Kiru:
Kwalliya wa ta dabi a ce wacce yawancin mutane masu hankali suke kalla su yaba ko ba dan su aka yi ba. Duk namijin da matarsa tayi masa kwalliya amma bai yaba ba dole akwai rashin jin dadi daga bangaren mata da kuma dalilin hakan da mijin, dalin sun hada da; Watakila yanayi na rayuwa, Rashin sanin mahimmancin hakan daga namiji, Kallon/Tunanin wasu a waje, Rashin girmama juna. Abin da ke haifar wa shi ne; Zai kawo rashin jituwa, Zargi daga bangaren matar, Tunanin yin mu’amala da wasu Mazan. Hanyar da za a magance matsalar ta hanyar Fahimtar juna, Ta kulawa da bukatun juna, Ta daina zarge-zarge da tuhuma daga bangaren matar. Daga bangaren maza kuma; Sanin girman Allah, Ba da cikakken lokaci, yabawa, kyauta da dai sauransu. Allah ya ba da Sa’a.
Hassana Labaran Danlarabawa daga Jihar Kano:
Wannan abu yana ci wa mata tuwo a kwarya! Saboda mace za ta zage ta yi kwalliya mai kyau, ta bata lokaci wajen shafe-shafe ta sanya sutura mai kyau. Amma wani abin takaici idan miji ya dawo ko kallo ba ta ishe shi ba, balle furucin yabo ya fito daga bakinsa. Dalilai da hujjojin da suke kawo hakan suna da yawa, amma ga kadan daga ciki; Wasu mazan girman kai ke hana su yabawa, Wasu suna ganin idan suka yaba kamar hakan zai jawo matan su raina su, wanda kuma ba hakan ba ne, Wasu kuma miskilanci ne, a ransu sun yaba amma ba za su iya furtawa da baki ba. Hakan zai iya haifar da abubuwa da dama, misali; yawan samun sabani a zamantakewar aure, domin ita mace tana son ta yi abu mijinta ya yaba mata. Sannan idan miji ba ya yaba kwalliyar matarsa watarana matar za ta gaji ta daina, idan ya dawo ya ganta tagajan-tagajan babu kintsi balle gyara, idanu duk kwantsa hammata na samami, kaya dukun-dukun, idan za ta fita unguwa sai ta fesa wanka da kwalliya, mazan waje su more wa kallonta, kun ga an haifi da mara ido kenan.
Mata za su iya gyara matsalar ta hanyar nuna wa mazajensu rashin jin dadin su kan nuna rashin kulawa da yabawa idan sun yi kwalliya. Ta hanyar shagwaba da kissa da nuna masa cewar domin shi fa kika yi, idan ya yaba za ki ji dadi. Wataran ma idan kika ga bai yi magana ba za ki iya mikewa a gaban shi ki jujjuya ki kashe ido da murya ki ce masa, “Sweety na yi kyau kuwa?” Ina tabbatar miki ko bai yi niyyar yabawa ba take zai ba ki amsa da, “Kwarai kuwa, kin yi kyau Honey.” Shawarata gare ku maza; ku kasance ma su yaba kwalliyar matanku, domin don ku suke kwashe lokaci su yi, yabawar za ta dadada musu rai su san ba aikin banza suke yi ba, kuma hakan zai kara dankon kauna. Abin alfaharinka ne a ce ka dawo gida ka tarar da matarka das da ita, ta sha wankan sukari tana jiran ka. Me ya fi wannan dadi? Babu abin da za ka saka mata da shi irin ka yaba kwalliyar, za ta ji ta a lokacin tamkar wata sarauniya. Ina fatan maza za su dauki wannan shawara, domin ci gaba da samun dorewar zaman lafiya tsakaninsu da matayensu.
Abdullahi Adamu Gwani (Mai Nasara):
Kwalliya wa ta dabi’a ce da duk hallita suke yi don tsabtace kai, birge abokan mu’amala ko don kasancewa cikin annashuwa da cikakkiyar lafiya. Masana sun tabbatar cewa babu wanda ya fi mace son idan tayi abu a yaba ballantana ma tayi kwalliya don abin muradinta (Minanta), idan ko ba ta samu yabo ko nuna an gamsu ba! Dole ta kasance cikin bacin rai. Abubuwan dake janyo hakan; Yau da kullum, Karancin ilmin zamantakewar aure, Gajiya/Damuwa. Zai Iyya haifar da; Rashin jituwa, Zarge-zarge, Rashin kwanciyar hankali da kuma mutuwar aure. Hanyoyin da za a magance matsalar Kamar su; Samin ilmin zaman takewa, Yiwa juna uzuri, Mace ta saurari mijinta a lokacin da yake jawabi, Rage korafi a kai-a-kai, Bawa mai gida hakuri bayan an yi masa kuskure da sauransu. Gareku maza; Tuna girman Allah, Yaba abubuwan da aka yi don kai, Tukuici ga mace, Yafiya.
Mujittaba Ya’u Ali B/prp Nasarawa LGA Kano:
Dalilin da yasa mazajensu ba sa yabawa shi ne rahin zaman lafiya, ko kuma auren da babu soyayya. Hakan zai haifar da rashin tausawa juna, sannan da rashin ganin girman juna. Hanyar ita ce tarairaya da nuna jinkai da tausayawa da kuma kulawa da mujin a ko da yaushe. Shawara anan shi ne; Ya zamo Mace a ko da yaushe ta kasance mai hakuri da juriya da rikon amanar mijinta, sannan ta zamo mai duba me mijinta ya fi so dan ta yi masa.