ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Najeriya Ya Yi Maraba Da Isowar Jirgin Ruwan Farko A Tashar Jiragen Ruwa Da Ke Ruwa Mai Zurfi Ta Lekki

by CMG Hausa
4 years ago
Lekki

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi maraba da samun nasarar isar jirgin ruwan farko zuwa tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, wacce ita ce tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta farko a kasar da ake gudanar da aikin gina ta a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.

Babban jirgin ruwan dakon kaya mai samfurin ZHEN HUA 28, ya taso ne daga yankin Hong Kong na kasar Sin, ya kuma isa kasar Najeriya a ranar Juma’a, wanda ke dauke da manyan injuna guda 3 da ake amfani da su wajen loda kayayyaki daga jiragen ruwa zuwa gabar teku, da wasu manyan injuna guda 10 da ake amfani da su wajen sauke kwantainoni daga cikin manyan jiragen ruwan dakon kaya a gabar teku, kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana ta bakin mai taimaka masa a fannin yada labarai Femi Adesina.

  • Kotun Daukaka Kara Ta Daure Sanata Nwaoboshi Shekara 7 Bisa Laifin Almundahana

Shugaban Najeriyar ya taya murna ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin sufuri ta ruwan kasar, inda ya bayyana cewa, amincewa da ya yi na gina sabbin tashoshin jiragen ruwa guda hudu a kasar, ciki har da tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

ADVERTISEMENT

A cewar sanarwar, matakin zai kuma taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi masu tarin yawa, da janyo jarin kasashen waje, da kuma kara azama kan yin kasuwanci cikin sauki a kasar.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, amfanin teku da amfanin ruwa suna da matukar muhimmanci ga inganta zaman rayuwar al’ummar Najeriya, don haka a cewarsa, gwamnati za ta yi iyakar kokarinta wajen bunkasa fannin don kyautata makomar fannin.(Ahmad)

LABARAI MASU NASABA

An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

Lekki
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”
Daga Birnin Sin

An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

July 27, 2026
Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9
Daga Birnin Sin

Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

July 27, 2026
Ribar Manyan Kamfanonin Sarrafa Kayayyaki Na Sin Ta Karu Da Kaso 18.7 A Rabin Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Kamfanonin Sarrafa Kayayyaki Na Sin Ta Karu Da Kaso 18.7 A Rabin Farkon Bana

July 27, 2026
Next Post
Muna Yin Siyasa Ce Bisa Tsammanin Gaba Za Ta Yi Kyau –Hajiya Halimah

Muna Yin Siyasa Ce Bisa Tsammanin Gaba Za Ta Yi Kyau –Hajiya Halimah

LABARAI MASU NASABA

Lekki

WAFU B 2026: Nijeriya Ta Doke Ghana Da Ci 4-2 A Wasan Farko

July 27, 2026
An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

July 27, 2026
Lekki

NSCDC Ta Cafke Mutane 2 Da Ake Zargi Da Sace Kayan Titin Jirgin Kasa A Kano

July 27, 2026
Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

July 27, 2026
Lekki

Obi-Kwankwaso Obasanjo Yake Goyon Baya, Amma Atiku Zai Iya Lashe Zabe – Momodu

July 27, 2026
Ribar Manyan Kamfanonin Sarrafa Kayayyaki Na Sin Ta Karu Da Kaso 18.7 A Rabin Farkon Bana

Ribar Manyan Kamfanonin Sarrafa Kayayyaki Na Sin Ta Karu Da Kaso 18.7 A Rabin Farkon Bana

July 27, 2026
Xi: Sin Ta Shirya Kara Karfafa Dangantaka Da Brazil

Xi: Sin Ta Shirya Kara Karfafa Dangantaka Da Brazil

July 27, 2026
Tinubu Ya Goyi Bayan Kafa Sabon Asibitin Koyarwa A Bichi — Ɗan Majalisar Kano

Tinubu Ya Goyi Bayan Kafa Sabon Asibitin Koyarwa A Bichi — Ɗan Majalisar Kano

July 27, 2026
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 30, Sun Ƙone Gidaje Da Shaguna A Kaduna 

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 30, Sun Ƙone Gidaje Da Shaguna A Kaduna 

July 27, 2026
Kwalejin Kimiyya Ta Kogi Ta Dakatar Da Malamai Kan Zargin Lalata Da Ɗalibai Da Sauran Laifuka

Kwalejin Kimiyya Ta Kogi Ta Dakatar Da Malamai Kan Zargin Lalata Da Ɗalibai Da Sauran Laifuka

July 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.