• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Yarda Da Kai Ya Sa Wasu Kasashen Yamma Ke Neman Ta Da Matsaloli

by CMG Hausa
3 years ago

Ofishin babban kwamishina mai kula da aikin kare hakkin dan Adam na MDD ya gabatar da wani rahoto dangane da jihar Xijiang ta kasar Sin a kwanan baya, wanda ya nuna al’adar kasar Amurka da wasu kawayenta ta neman yin amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin wani makami.

Me ya sa a ce haka?
Saboda da farko dai, yadda aka tsara rahoton ya saba ka’idoji. A matsayinsa na daya daga cikin hukumomin MDD, ya kamata ofishin babban kwamishina mai kula da hakkin dan Adam ya gudanar da duk wani aiki ne bisa iznin da majalisar kare hakkin dan Adam ta ba shi, kuma ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata kasa ba.

  • Neman Illata Kasar Sin Ya Haifar Da Matsalar Tattalin Arziki Ga Amurka

Amma ofishin ya gabatar da wannan rahoto kai tsaye, ba tare da neman samun izini ba, kuma bai taba neman sauraron ra’ayin Sin ba. Kana ta wannan hanya ya tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin.

Na biyu, shi ne bayanan dake cikin rahoton sun saba da sanarwar da Madam Veronica Bachelet, babbar kwamishinar mai kula da aikin kare hakkin dan Adam ta MDD, ta gabatar, a ranar 28 ga watan Mayun bana, bayan da ta kammala ziyararta a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Inda ta yaba da kasar Sin, kan kokarinta a fannonin rage talauci, da kare mutane marasa karfi, da yunkurin tabbatar da ingancin hakkin dan Adam, da dai sauransu.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Hakika idan mun yi nazari kan mutanen da suke aiki a ofishin babban kwamishina mai kula da aikin hakkin dan Adam, za a fahimci cewa, zai yi wahala wannan ofishi ya gabatar da wani rahoto na gaskiya.

Saboda kasar Amurka da wasu kawayenta sun tura ‘yan korensu don su zama manyan jami’an ofishin, inda su kan yin amfani da wasu bayanai marasa gaskiya wajen tsara rahotannin da suke haifar da matsin lamba ga kasar Sin, da sauran kasashe masu tasowa.

Amma me ya sa kasar Amurka da abokanta ke kokarin yin amfani da damammaki daban daban wajen shafa kashin kaza ga kasar Sin, da kafa shingaye ga sauran kasashen masu tasowa?

A ganina, suna haka ne domin ba su yarda da kansu ba.
Kasashen yammacin duniya na ganin cewa, dole ne kasashe masu tasowa su bi tsarin dimokuradiya irin nasu, da zama karkashin jagorancinsu, kafin su iya samun ci gaba mai dorewa.

Sai dai kasar Sin, a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta zabi hanyar da ta tsara da kanta kuma da dace da yanayin al’ummarta, inda ta dauki tsarin gurguzu mai siffar musamman ta Sin, tare da samun babban ci gaba, cikin gomman shekarun da suka wuce.

Wannanya sa kasashen yamma kaduwa, saboda yadda kasar Sin ta samu nasara ta nuna cewa, kasashe masu tasowa za su iya raya kansu, ta hanyar musamman da suka zaba, maimakon ci gaba da bin umarnin kasashen yamma.

Wannan damuwa ta sa kasar Amurka da wasu kawayenta ke kokarin gogayya da kasar Sin, da haifar da matsaloli a harkoki masu alaka da hakkin dan Adam, da jihar Xinjiang, da yankin Taiwan na kasar Sin, da dai sauransu, don hana kasar Sin samun ci gaba. Sai dai kasar Sin ta yi ta samun nasarar daidaita wadannan matsaloli, bisa cikakken imanin da take da shi a kan turbar da ta zaba. Haka kuma Sinawa suna iya hakuri da mabambantan ra’ayoyin da ake samu a duniya, da iya tinkarar duk wani kalubalen da suka kunno kai yayin da suke kokarin raya kasarsu.

A nasu bangare, kasashe masu tasowa su ma sun fara ganin yanayin rashin adalci na tsare-tsaren kula da harkokin duniya da kasashen yamma suka gabatar, wannan ya sa suke kokarin nemo hanyar raya kansu wadda ta dace da yanayin da suke ciki.

Wannan wani muhimmin yanayi ne da muke fuskanta a wannan zamanin da muke ciki. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Bene Ya Rufta Da Mutum Tara A Jihar Legas

Bene Ya Rufta Da Mutum Tara A Jihar Legas

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.