Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya misalta rasuwar Sarkin Funakaye, Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga III a matsayin babban rashin ba kawai ga masarautarsa ba har ma ga jihar da ma kasa baki daya.
Sarkin na Funakaye ya rasu ne a ranar Asabar 27 ga watan Agustan 2022 yana da shekaru 45 a duniya.
Gwamnan da yake magana kan rasuwar na Sarkin, ta cikin sanarwar manema labarai da kakakinsa Malam Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce jihar Gombe ta yi rashin hazikin Sarki wanda ya himmatu wajen bunkasa zaman lafiya, hadin kai da cigaban jihar da ma kasa baki daya.
Ya ce watanni 16 da ya yi a matsayin Sarkin ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kai da cigaban jihar.
Daga bisani ya mika sakon ta’aziyyarsa a madadin gwamnati da al’ummar jihar ga iyalan Sarkin da Masarautar Gombe da makusantan mamacin hadi da fatan Allah zai bai wa al’ummar jihar hakuri na wannan rashin.
Ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya sanya shi cikin Aljanna Madaukaka.
Wakilinmu ya labarto cewa marigayi Alhaji Muazu Muhammad Kwairanga ya zama Sarkin Funakaye ne bayan da gwamnan Jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ya nada shi a watan Mayun 2021.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp