Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa a taron dumamar yanayi na duniya (COP28), wanda ya gudana a Kasar Dubai.
Sai dai, ana ta faman caccakar gwamnatin tarayya dangane da yawan tawagar da suka wakilci Nijeriya a wannan babban taron.
- An Bayyana Rawar Da Kasar Sin Ta Taka Kan Sauyin Yanayi Yayin Taron COP28
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
An rawaito cewa, Kasar Nijeriya ta tura wakilai har mutum 1,411, wadda ta kasance kasa ta uku a yawan kasashen da suka tura, domin halartar wannan taro.
Lamarin ya gamu da suka kwarai da gaske, musamman ganin yadda al’ummar Nijeriya ke ta fama da halin kaka-na-ka-yi, sakamakon halin matsatsin rayuwa da aka samu kai a ciki, tun bayan janye tallafin mai, inda masu ruwa da tsaki kuma suka soki matakin Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu; kan wannan lamari.
A gefe guda kuma, Fadar Shugaban Kasa ta yi karin haske a kan wakilai 1,411, inda ta ce wadanda gwamnatin tarayya ta dauki nauyi, ba su kai mutum 100 a cikinsu ba.
Da yake tofa nasa albarkacin bakin, Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Tinubu da yin amfani da wannan taro na sauyin yanayi zuwa taron jam’iyya, a daidai irin wannan lokaci da al’ummar Nijeriya ke neman tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Abubukar, a wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Kakakinsa, Paul Ibe, ya kuma zargi Tinubu da barnatar da dukiyar kasa; duk kuwa da halin matsin da kasar ke ciki. Ya kara da cewa, duk gwamnatin da ta san abin da take yi, musamman a irin wannan lokacin, ba za ta taba fara yin yunkurin tura wakilai har sama da dubu wani taro ba.
Haka nan shi ma dan takarar Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana yawan wakilai a matsayin asarar dukiyar al’ummar kasa.
A shafin Obin na Tiwita, ya ce, mafi yawan wadanda aka tura a matsayin wakilan, ba su da wata alaka da aikin gwamnati.
“Mafi yawan wadanda aka tura, babu abin da suka sani dangane da sauyin yanayi,” kamar yadda ya zarga.
Sannan, ya yi tir da matakin da cewa; a irin lokacin da al’ummar Nijeriya ke kan gwagwarmayar neman abincin da za su kai baki tare da matsin rayuwa da ya yi musu katutu, sai ga shi wannan gwamnati ta kwashi makuden kudade ta tura tulin wakilai zuwa wani taro a kasar waje.
Da yake mai da nasa martanin, babban mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren yada labarai, Temitope Ajayi, a wata sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa; ba dukkanin wakilan Nijeriya 1,411 a taron COP28 ne gwamnati ta dauki nauyinsu ba.
Ya ce, wakilan Nijeriya sun hada da bangarorin fararen hula, shugabannin ‘yan kasuwa, kwararru a bangaren muhalli, masana kan yanayi, ‘yan jarida da kuma jami’an gwamnati daga ma’aikatu da sassa daban-daban.
Duk da dai, bai bayyana adadin jami’an da gwamnatin ta dauki nauyin biyan kudin tafiyar tasu taron ba, sabanin jita-jitan da ake cewa; sun kai sama da wakilai 600 da gwamnati ta dauki nauyinsu.