A yayin da kasashe masu tasowa ke fuskantar wariya kamar wata saniyar ware daga takwarorinsu na kasashen yamma da Amurka a gefe guda, sai ga wata guguwa mai karfi dauke da hadin gwiwar kasashen BRICS ta taso da nufin samar da daidaito, ‘yancin kasashe masu tasowa tare da kiran sauya fasali a tsare-tsaren yadda ake gudanar da harkoki na kasa da kasa.
Wannan guguwa ta yi nasara sosai, inda taron kolin kungiyar BRICS na bana karo na 17 da aka yi a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, ya tayar wa shugaban Amurka da hankali, wanda ya yi barazanar kara kakaba harajin kaso 10% kan kasashen dake goyon bayan sukar muradunta na “kama karya”. Wannan sai ya tuna min da wani karin maganar da Hausawa ke cewa, “wane dare ne, Jemage bai gani ba.”
- Babu Wanda Ya Buƙaci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC
- Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza
Yayin da yanayin dangantakar kasa da kasa ke fuskantar kalubale da sauye-sauye masu yawa, kasashen BRICS suna kara samun karbuwa a matsayin kungiya mai rajin yin kwaskwarima ga tsarin gudanar harkoki na kasa da kasa domin samar da duniya mai tattare da mutunta juna da adalci.
Duba da hakan ne, a yayin taron kolin, firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira da cewa, “ya kamata kasashen BRICS su zage damtse wajen ganin sun ci gaba da yin gyare-gyare a tsarin gudanar harkoki na duniya, kuma Sin a shirye take ta hada gwiwa da sauran kasashen BRICS, domin sa kaimi ga gudanar da harkokin duniya cikin adalci, da daidaito, da inganci da tsari, da yin aiki tare domin gina ingantacciyar duniya.”
Jawabin na Li ya sake jaddada aniyar kasar Sin na karfafa kasashen BRICS a matsayin babbar hanyar yin gyare-gyare kan tsarin gudanar harkokin duniya. A matsayinta na wakiliyar muryar kasashe masu tasowa, BRICS na tattare da burika na sauya fasalin yadda ake gudanar da harkokin kasa da kasa.
Shi ma Uban taro mai masaukin baki, shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana a jawabinsa na taron kolin cewa, “Idan har ba a samu sauyi a tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa a wannan karni na 21 ba, to ya zama wajibi kasashen BRICS su taimaka wajen ganin an sabunta shi.”
BRICS taska ce ta hadin kai, daidaito da kuma kokarin tafiya tare don samun ci gaba da tsira tare, da kuma karfafawa kasashe masu neman ‘yancin fadin albarkacin bakinsu a harkokin tsare-tsare na hadin kan kasashen duniya.
Taron kolin kungiyar na bana, na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwannin duniya ke cike da firgici biyo bayan yakin cinikayya da kasar Amurka ta kaddamar, amma BRICS ta tsaya tsayin daka wajen inganta harkokin tattalin arziki, inda kungiyar ke samar da wani dandali na bai daya da ke tallafawa cinikayya a kasashe daban-daban, da inganta cinikayyar a tsakaninsu, wanda hakan ya ba su damar bunkasa amfani da kudaden cikin gida, don rage dogaro kan wasu kasuwanni masu iyaka.
Yayin da kasashe da dama ke nuna sha’awar shiga kungiyar, hakan na nuni da tasiri da nasarar da kungiyar ke samu cikin sauri, saboda ta bayyana gaskiya da adalci a fili, ta inganta tsarin dimokuradiyyar duniya, kowa yana da ‘yancin fadi a ji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp