Uwargidan shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da gudummawar Naira biliyan 1 don tallafawa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.
An bayar da gudummawar ne a ƙarƙashin muradun gwamnatin Tinubu na sabunta fata wanda uwargidan shugaban kasa ta jagoranci kaddamarwa a jihar domin aikin agaji.
A yayin ziyarar jaje da ta kai jihar a ranar Talata, uwargidan shugaban kasar ta gabatar da kudin da kayan agajin ga gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a Minna, babban birnin jihar.
Cikakken bayanai daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp