Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu, ta tabbatar da cewa bambance-bambancen Halsuna da muke da shi a Nijeriya, shine musabbabin karfin kasar.
Ta ce ta hanyar rayuwa cikin kwanciyar hankali da soyayya ne za a iya aiwatar da Basira da Hikimar da ubangiji ya bamu a tsakaninmu.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi ya fitar, ya ce, Remi Tinubu, ta yi wannan furucin ne a wajen rabon kayan agaji da sake tsugunar da iyalai 500 da rikicin kabilanci ya shafa a kananan hukumomi shida na jihar Filato.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya yabawa uwargidan shugaban kasa kan nuna cewa, ita uwa ce ta gaskiya.
Kimanin iyalai 500 da aka zabo daga kananan hukumomin Mangu, Riyom, Barkin Lado, Bassa, Bokos da Jos ta Kudu na jihar sun samu Naira miliyan daya kowannensu domin su koma yankunansu su sake gina gidajensu.