• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ribar Dala Miliyan 240: ‘Yan Kasuwa Na Zargin CBN Da NNPC Da Take Musu Hakki

by Sulaiman Bala Idris
3 years ago
CBN

‘Yan kasuwan mai daga kamfanin Canaf da BLCO da sauran wasu masu hada-hadar kasuwancin man fetur sun gudanar da zanga-zanga kan zargin kamfanin mai na kasa (NNPC) da babban bankin Nijeriya (CBN) wajen kawo tsaiko kan biyansu kudadensu.

Zanga-zangar ta gudana ce a ranar Laraba da ta gabata, inda suka yi dafifi a harabar shalkwatan kamfanin NNPC da ke Abuja, inda suke ta daga kwalaye masu dauke da rubutu daban-daban da ke nuna a biyasu ribarsa tare da cewa shugaban kasa yana sane da kasuwancin da suke gudanarwa.

  • Sabon Kamfanin Mai Na NNPC Zai Ceto Makamashin Nijeriya

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban tawagar, Mohammed Abubakar ya ce, “Mu ne wakilan da ke sayar da danyan man Nijeriya ga kamfanoni masu matatun mai.”
A cewar Abubakar, suna gudanar da zanga-zangar ne domin NNPC ta baya su kudaden a kan dala biyu ga kowacce gangan mai.

“Shugaban kasa ya amince da gudanar da kasuwancinmu tun a shekarar 2018. Muna so tsohuwar NNPC ta biya mu ba sabuwa ba.”

Ya yaba wa jami’an tsaro wajen samar musu da tsaro lokacin da suke gudanar da zanga-zangan tun lokacin da suka fara har zuwa 8 ga watan Yulin 2022, lokacin da Sufeton ‘yan sanda na kasa, IGP Usman Baba ya bukaci su dakatar da zanga-zangar.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

Sun bayyan akwai cikakken hujja da ke nanu cewa NNPC da CBN da gangan suka ki biyan kudaden.
“Shugaban kasa ya amince da a biya mu wadannan kudade na riba a hukumance bisa kasuwancin da kamfanonin BLCo LPFO da kuma LNG suka gudanar.

“Muna gudanar da wannan zanga-zangar ne domin sanar da duniya cewa NNPC da CBN suna amfani da sunan shugaban kasa wajen kokarin cin kudin ba tare da sanin shugaban kasa ba.”

Kamfanin ya gudanar da yarjejeniya a ranar 28 ga watan Satumbar 2021, inda ya samu amincewar karamin ministan mai, wanda ya nuna wa ‘yan jarida. Yarjejeniyar mai take, “Mu kamfanin Canaf mun saka hannun yarjejeniya da jami’anmu, Mista Anthony Awa Mba da Mista Mohammed Abubakar domin kawo mai ga tare da BLCo da dukkan sauran abubuwan da suka shafi man fetur a Nijeriya.

“Bayan kammala dukkan hada-hadar kasuwancin, mu kamfanin Canaf mun bukaci a biya mu game da wannan kasuwanci wanda muka tura asusun banki kai-tsaye ga NNPC da fadar shugaban kasa nan take.”

Shugaban kamfanin, Mista Okwii Modekwe yana kira da kamfani NNPC da ta biya ‘yan kasuwan dala miliyan 240 daga cikin dala biliyan daya na kasuwancin da suka rattaba hannu tun a ranar 19 ga watan Yulin 2018.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025
Labaran Kasuwanci

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya
Labaran Kasuwanci

Kuratan Sojoji 1,196 Aka Yaye A Makarantar Horar Da Sojoji Ta Zariya

June 21, 2025
Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman
Labaran Kasuwanci

Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman

January 11, 2025
Next Post
An Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Cinikayya Da Raya Tattalin Arziki Ta Dalar Amurka Miliyan 170 Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka

An Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Cinikayya Da Raya Tattalin Arziki Ta Dalar Amurka Miliyan 170 Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka

LABARAI MASU NASABA

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.