Ma’aikatar yada manufofin kwamitin kolin JKS ta kira taron ganawa da manema labarai game da “Shekaru goma na kasar Sin” yau da safe, babban sakataren hukumar kula da kadarori mallakar gwamnatin kasar ta majalisar gudanarwar kasar Sin, kana kakakin watsa labaran hukumar, Peng Huagang, ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2012 wato bayan da aka kira babban taron wakilan JKS karo na 18, kamfanoni mallakar gwamnatin kasar suna sauke nauyin dake bisa wuyansu a bangarorin tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar al’umma, haka kuma suna taka babbar rawa wajen cimma burin samun wadata tare a fadin kasar.
Ya zuwa karshen shekarar 2021, gaba daya adadin darajar kadarorin manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta kasar ya kai kudin Sin yuan triliyan 75.6, adadin da ya karu da kaso 141.1 bisa dari idan aka kwatanta da na karshen shekarar 2012, kana adadin ribar da suka samu tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2021 ya kai kudin Sin yuan triliyan 15.7, wato kowace shekara adadin yana karuwa da kaso 8 bisa dari.
A bayyane an lura cewa, manyan kamfanonin suna ba da gagarumar gudunmowa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)