• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Richard Sears: Harufan Sinanci Ba Kawai Na Kasar Sin Ba Ne, Al’ada Ce Mai Daraja Ga Duniya Baki Daya

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Harufan Sinanci

Wasu harufan Sinanci

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ranar 20 ga watan Afrilun kowace shekara, rana ce ta harshen Sinanci da MDD ta tsai da. A halin yanzu da kasar Sin ke ta kara mu’amala da kasashen duniya, al’ummun kasashe daban daban ma na kara sha’awar koyon Sinanci, kuma Richard Sears, wani masani dan kasar Amurka na daya daga cikinsu.

Richard Sears yanzu haka yana zaune a birnin Nanjing, hedkwatar lardin Jiangsu na kasar Sin, kuma ya shafe shakaru da dama yana nazarin harufan Sinanci, har ma ya kafa wata ma’adanar bayanai na harufan Sinanci na ainihi. A ganinsa, harufan Sinanci ba kawai na kasar Sin ba ne, domin kuwa su wata al’ada ce mai daraja ga duniya baki daya.

  • Za A Yi Taron Koli Tsakannin Kasar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya A Watan Mayu A Xi’an

Gano sirrin da ke kunshe a cikin harufan Sinanci abu mafi ban sha’awa ga Richard Sears. A ganinsa, harufan Sinanci na da tsawon tarihi na dubban shekaru, don haka, kowanensu na tattare da sirri na yadda al’ummar gargajiya ke fahimtar abubuwan duniya, kuma ya kamata a yi nazari a kan tarihinsu a kimiyyance, don a san daga ina ne suka fito, ta yadda za a gane sauye-sauyensu, ta yin nazari a kan ainihin lafazinsu da ma rubutunsu.

A ganinsa, in dai an san asalin harufan Sinanci, lallai za a samu damar fahimtar rayuwar al’ummar Sinawa a zamanin gargajiya da ma al’adunsu. Misali, akwai harufa da suka nuna yadda ake ayyukan saka a zamanin gargajiya, akwai kuma wasu da suka nuna yadda aka gudanar da ayyukan gona da kiwon dabbobi a da. To, idan ba a yi kokarin fahimtar labaran da ke kunshe a cikin harufan Sinanci ba, da wuya a samu fahimtar ainihin al’adun gargajiya na kasar Sin.

Harufan Sinanci
Richard Sears, wanda ya shafe shakaru da dama yana nazarin harufan Sinanci, har ma ya kafa wata ma’adanar harufan Sinanci na ainihi

Richard Sears ya ce, yana matukar jin dadin nazarin harufan Sinanci. “In na koyi wani sabon abu, hakan ya kan faranta mini rai, don haka, ina ta koyon harufan Sinanci, kuma duk lokacin da na gano wani sabon labarin da ke ciki, na kan yi farin ciki sosai.”

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

A shekarar 1994, ciwon zuciya na ba zata ya same shi, lamarin da kuma ya sa ya fara tunanin ma’anar rayuwa, don haka, ya yanke shawarar shigar da dukkanin harufan Sinanci na gargajiya da ke cikin wasu littattafan gargajiya na kasar Sin, game da harufan Sinanci a cikin kwamfutar sa, don ya kafa wata ma’adanar bayanai ta harufan Sinanci na asali. Ya ce, “Dole in samu littattafan da suka dace mu dogara da su, kuma in saurari ra’ayoyi na mabambantan masana, sa’an nan in yi tunani da kaina, don a samu harufan Sinanci na ainihi. Don haka, dole ne in kafa wata tashar yanar gizo, kuma in kafa wata ma’adanar bayanai, don haka, na fara yin nazari a kan harufan Sinanci da ake amfani da su a yau da kullum, kuma na kafa wata ma’adanar bayanai.”

Bayan da ya shafe tsawon shekaru takwas, a shekarar 2002, Richard Sears ya kaddamar da ma’adanar bayanai da ke kunshe da harufan Sinanci sama da 6500 a shafin yanar gizo, kuma masu ziyartar shafin na iya bincika mabambantan salon rubutu na wadannan harufan Sinanci, tare da fahimtar sauye-sauyensu. Ya zuwa yanzu, wadannan harufan Sinanci da ke cikin wannan ma’adanar bayanai sun karu har zuwa kimanin dubu 100. Ya ce, “Na tattara harufan Sinanci na gargajiya kimanin dubu 100, kuma ya zuwa yanzu, na yi nazari a kan wasu dubu 15, da aka fi yin amfani da su a rayuwar yau da kullum, kuma burin da nake neman cimmawa shi ne in samar da cikakken bayani a kan asalin kowane harafin Sinanci.”

Harufan Sinanci
Ga yadda Richard Sears yake gabatar da jawabi a gun wani taron kara wa juna sani game da harufan Sinanci na asali

A ganin Richard Sears, ba kawai domin a iya Sinanci ne a ke koyon sa ba, a’a ana koyon sa domin a samu damar fahimtar al’adun kasar Sin da ke da tsawon tarihi na dubban shekaru. Ya ce, yadda mabambantan mutane ke fahimtar al’adu ya kan sha bamban, kuma wannan fahimta muhimmin mataki ne na kawar da nuna bambanci tare da cimma daidaito. “Ina ganin labaran da ke cikin harufan Sinanci suna da ban sha’awa, shi ya sa duk harafin Sinanci da na duba, na kan yi nazari a kan labaran da ke ciki. Amma in wasu suka duba, su kan ga irin salon rubutunsa daban daban, wadanda suke ba su sha’awa sosai. Mu kan ce “Ra’ayi riga, kowa da irin ta sa”, don haka ma mabambantan mutane ke da ra’ayoyi mabanbanta.”

Richard Sears, ya gane ma idonsa yadda karin jama’a ke sha’awar koyon Sinanci. Ya ce, a yayin da kasar Sin ke ta kara bude kofarta ga duniya, tasirinta, da ma matsayinta a duniya na dada inganta, lamarin da ya sa sassan kasa da kasa ke fatan kara fahimtarta, kuma ko shakka babu, harshen Sinanci wani mabudi ne na sanin kasar. Yana mai cewa, “A kasar Amurka, ana iya jin Sinanci a makarantun sakandare, da ma jami’o’i da dama, inda wasu ke koyar da harshen, wasu kuma ke koyo, ta haka muke iya gane yadda harshen Sinanci, da ma harufansa ke kara tasirinsu a duniya. Yanzu haka, kimanin kaso 20% na al’ummar duniya na magana da yaren Sinanci, a yayin da kaso 20% ke bayyana ra’ayoyinsu da harufan Sinanci, kuma hakan abu ne mai matukar muhimmanci. Idan kana son fahimtar abin da wani basine ke tunani, ya fi kyau ka koyi Sinanci.”

A ganin Richard Sears, koyon harufan Sinanci ta hanyar nazarin asalinsu, hanya ce ta mai da wannan harshe mai matukar wahala ya zama kananan labarai, ta yadda mai koyo zai iya rike shi ta hanyar fahimtarsa, kuma ta haka za a kara fahimtar bambancin al’adu a tsakanin kasar Sin da kasashen yamma, kana al’ummar kasashen ma za su kara jin saukin mu’amala da juna. Ya ce, harufan Sinanci ba na kasar Sin kawai ba ne, harufa ne na duniya baki daya. “Harufan Sinanci ba na kasar Sin kawai ba ne, harufa ne na duniya baki daya. An shafe kimanin shekaru 5000 ana amfani da harufan Sinanci a kasar Sin, don haka, ba abu ne na yanzu ba, harufa ne da ke da tsawon tarihi na shekaru 5000, wadanda ke da tasiri ga duniya.

Harufan Sinanci
Ga yadda Richard Sears yake tare da dalibai a jami’ar koyon ilmin malanta na lardin Henan

Lokacin da mutanen daular Roma ta gargajiya suka zo kasar Sin, da Larabawa da suka zo, dole ne su koyi Sinanci. Harufan Sinanci ba kawai suna da tasiri ga kasar Sin kadai ba ne, tasirin su ya shafi duniya baki daya, don haka ma suka kasance wani bangare na al’adun duniya.”

Richard ya ce, koyon harufan Sinanci na da wahala ga wasu baki, amma in an koya, za a ga cewa, Sinanci yana da ban sha’awa sosai, ya ce, “Koyon harufan Sinanci ba shi da sauki, dole a jure, a kan kwashe wasu shekaru kafin an iya karatu. Na kan ce ma baki matasa, in ka fara koyon harufan Sinanci daga yanzu da kake da shekaru 20, kuma ka yi kokari, to, a lokacin da ka kai shekaru 25, za ka iya karatu, amma idan ba ka yi kokari ba, to har zuwa lokacin da ka kai shekaru 25, ba za ka iya ba. Na kan karfafa gwiwar baki da su koya ba tare da tsayawa ba, kuma idan an shafe wasu shekaru, tabbas za a cimma nasara.”

Harufan Sinanci
Yadda ake halartar bikin ranar harshen Sinanci ta MDD a kasar Slovenia

Yanzu haka Richard ya kai shekaru 73 da haihuwa, kuma har yanzu yana ta nazarin harufan Sinanci tare da koyon kimiyya. Ya ce abin da yake fata shi ne ya rika fadakar da al’umma a kan yadda harufan Sinanci suka yi ta sauyawa daga asalinsu, ta yadda duk wani mai koyon harshen zai fahimci labaran da ke cikin kowane harafin Sinanci, da ma al’adu na musamman na kasar ta Sin.
(Lubabatu Lei)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mutum 14 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Bauchi

Next Post

Rikicin Sudan: Tsaka Mai-wuyar Da ‘Yan Nijeriya Suka Shiga

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

3 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

10 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

12 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Sudan

Rikicin Sudan: Tsaka Mai-wuyar Da 'Yan Nijeriya Suka Shiga

LABARAI MASU NASABA

Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

May 15, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

May 15, 2025
Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa

Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa

May 15, 2025
An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

May 15, 2025
NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC

NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC

May 15, 2025
Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu

Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu

May 15, 2025
Lassa Da Shawara Sun Kashe Mutum 183 A Jihohi 36 Da Abuja

Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC

May 15, 2025
Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

May 15, 2025
ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

May 15, 2025
‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.