Zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar Rivers ranar 30 ga Agusta, 2025 ya gamu da ruɗani, bayan da wasu fitattun ‘yan jam’iyyar PDP suka bayyana a matsayin ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi ƙarƙashin jam’iyyar APC a wasu yankuna.
A cewar rahoton LEADERSHIP, daga cikin ƙananan hukumomi 23 na jihar, a kalla 12 daga cikinsu na da ‘yan PDP da suka fito a matsayin ‘yan takarar APC, ciki har da Asari Toru, Ikwerre, Khana, Tai, Degema, Bonny, Oyigbo, Omuma, Ogu/Bolo, Gokana da Etche.
- Tinubu Ya Sasanta Wike, Fubara, Da Ƴan Majalisar Ribas
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Nijeriya Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 5 A Ribas
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin waɗanda suka yi nasara a baya a jam’iyyar PDP yanzu sun fito a ƙarƙashin tutar APC, lamarin da ya ƙara tayar da ƙura a siyasar jihar. A halin yanzu kuma, akwai alamun cewa jam’iyyu da dama ciki har da ADC, APP da wani ɓangare na APC na shirin ƙauracewa zaɓen.
A baya dai APP da ke da goyon bayan tsohon gwamna Siminalayi Fubara, ta lashe kujeru 22 daga cikin 23 a zaɓen watan Oktoba 2024, amma kotun ƙolin ƙasa ta rushe nasarorin saboda kuskuren hukumar zaɓe ta RSIEC da ta ƙasa ta bada sanarwar zaɓe cikin wa’adin kwana 90 da doka ta tanada.
Kakakin jam’iyyar ADC a jihar, Chief Luckyman Egila, ya ce har yanzu ba su yanke hukunci ba ko za su shiga zaɓen ko a’a ba, yayin da wani ɓangare na APC ke kokawa da rashin amincewar RSIEC da jagorancin jam’iyyarsu a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp