Rikici ya barke lokacin da wasu ‘yan daba suka farmaki gamayyar tawagar jami’an kula da Babbar Birnin Tarayya (FCTA) masu rasau a Lungu Crescent da ke yankin Wuse II a Abuja.
Rikicin ya barke ne lokacin da wasu mutane suka yi tawaye da rusan gine-ginen da jami’an suka fara a yanke wanda ya saba wa ka’idar hukumar FCTA, inda aka yi jina-jina a tsakanin tawagar jami’an da ‘yan daban.
- Buhari Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekaru 65
- Xi Jinping Ya Ci Gaba Da Halartar Taron Karba-karba Na Shugabannin Mambobin Kungiyar APEC Karo Na 29
An bayyana cewa ‘yan daban sun shirya yakin, sai dai tawagar jami’an tsaro sun yi kokarin tarwatsa su wanda ya haddasa tashin hankali.
Bayan faruwar lamarin, Jami’in gudanarwa da ke kula da Abuja da kewaye (AMMC), Umar Shuaibu ya bayyana cewa asalin filin wuri ne a ajiye motoci, amma masu wurin suka karya doka. Ya ce duk da wa’adin da hukumar gudanarwa ta FCT ta bayar kafin zuwa yin rusau din, amma masu wurin suka yi kunnen kashi kan daukar matakin da ya dace.
Shuaibu ya siffatna rusan wuraren shakatawa da ba sa kan ka’ida a matsayin matattaren ‘yan ta’adda wanda suke samun mafuka wajen farmakan mutane cikin dare.
Jami’in ya kara da cewa sashin bunkasa Babban Birnin Tarayya ba zai taba lamunta ba wajen barin mutane su yi gine-gine da ya saba wa ka’ida. Ya ce Abuja garin ne na doka da tsari kuma dole duk wanda yake zaune a birnin ya bi doka sau da kafa. A cewarsa, Ministan Abuja ya ba su ikon da umurni wajen tabbatar da an bi doka da oda.