Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wani dan bindiga mai suna Isah Lawal mai shekaru 33 da ya baro yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Lawal wanda ya kware a harkar fashi da makami, garkuwa da mutane, da satar shanu, an kama shi ne a wani samame da jami’an ‘yansanda karkashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal suka gudanar a jihar Kano a wani rahoton sirri da suka samu.
- Cire Tallafin Fetur: Ma’aikatan Jihar Jigawa Sun Ki Amincewa Da Karin Albashin Naira 10,000
- An Gudanar Da Bukukuwan Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Habasha Da Amurka Da Rasha
A ranar 4 ga watan Janairun shekarar 2024 ne aka kai samamen a karamar hukumar Karaye ta jihar da ke kan iyakar Kaduna da Kano, inda aka kwato shanu 55 da tumaki shida.
Dan bindigan Wanda ake zargin mazaunin kauyen Kaya ne da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, ya amsa cewa, ya tsere ne daga sansaninsu na ‘yan bindigar Maidaro da ke karamar hukumar Birnin Gwari sakamakon rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ‘yan sansanin.
Bayanin da Lawal ya yi a lokacin binciken, ya nuna cewa, ya koma jihar Kano musamman dajin Gwarzo-Karaye ne sakamakon mutuwar daya daga cikin shugabannin kungiyar, Bashir na Malumfashi a jihar Katsina, a yayin artabu da wata kungiyar ‘yan bindiga da ke hamayya da juna.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (DPPRO), ASP Abdullahi Hussaini, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya tabbatar da kama wannan dan ta’addan, ya yaba da kokarin jami’an ‘yansandan, ya kuma bayyana cewa, kwamishinan ‘yansandan, CP Mohammed Usaini Gumel, ya umurci a kara yawan jami’an ‘yan sandan da ke aiki kan iyakokin jihar don kare dukkan iyakokin jihar Kano.
CP Gumel ya nuna jin dadinsa da irin goyon baya da hadin kai da jama’ar jihar suka ba su, inda ya bukaci a ci gaba da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ‘yansanda mafi kusa.