Ministan Ma’adanai na Kasa, Dele Alake, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gano cewa ‘yan Nijeriya masu karfin fada a ji ne da ke da hannu wajen hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba ke daukar nauyin ‘yan bindiga da ta’addanci a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a a lokacin da yake kare kasafin kudin shekarar 2024 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai Kula da Ma’adanai cikin makon nan.
- Dalilin Da Yasa Ta’addanci Ke Ci Gaba Duk Da Kasafin Kudi Mai Gwabi Da Sojoji Ke Samu – Shugaban Tsaro
- Za A Shiga Mummunar Damuwa A Gaza Idan Ba Ku Dauki Mataki Ba – Gargadi Ga Majalisar Tsaro Ta MDD
Alake ya ce: “Wani binciken da muka gudanar ya yi nuni da cewa yawancin wannan rashin tsaro da ake fama da shi na ‘yan bindiga da ta’addanci yana da alaka da wannan bangare na masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
“Wadannan da kuke zaton ba ma’aikatanku ba ne, ko kuke ganin kamar ba mutanen da suke hakar zinariya a kasa ba ne, lallai ya kamata ku fahimta cewa su ne, sannan kuma, ‘yan Nijeriya masu karfin ikon fada a ji ne ke daukar nauyinsu ba wasu ‘yan kasashen waje bane. “Eh, za ku iya ganin baki da aka ajiye a matsayin wasu alamu na basaja, amma ba su ne tushen asalin aikin ba, ‘yan Nijeriya ne masu isa da iko wadanda suke goyon bayan wadancan ‘yan kasashen waje da kuke gani a kan tituna suke aiwatar da hakan.
“Wadanda ba su da karfi da suke aiki tare da masu aikin hakar ma’adinai, na basu damar kafa kungiyarsu ta hadin gwiwa domin kowane dan Nijeriya yana da hakkin rayuwa da bukatunsa, kuma idan har gwamnati ba za ta iya samar da wadannan abubuwa domin magance bukatu ba, to ba za mu iya ba da wannan shawara kuma mu tura ku cikin daji ba.”
Ya ce inganta tsaro a wuraren hakar ma’adanai da wuraren da ake son ya tabbata da kuma samar da aminci a fannin hakar ma’adinan kansa a Nijeriya zai dawo da masu zuba jari. Alake ya ce adadin ma’adanan da aka samar a Nijeriya ya haura Dala biliyan 700, inda ya ce kasar na da nau’in ma’adanai 44 da za a biya manyan bukatu, amma a halin yanzu ya zayyana guda bakwai kadai da suka zama mafi girman bukatu a duniya.
Shugaban kwamitin, Gaza Gbefwi, ya ce bangaren ma’adanai mafiya karfi ya kasance babban fata na karshe ga Nijeriya na samun nasarar bunkasar tattalin arzikin da ake bukata.