A fannin aikin gwamnati a Nijeriya, Rundunar ‘Yansandan Nijeriya (NPF) tana da tarihi wanda ya samo asali tun lokacin mulkin mallaka kuma ya tsaya a matsayin ginshikin tabbatar da doka da oda.
Sai dai kuma, a karkashin bajoji da riguna akwai rashin jin dadi a tsakanin masu sanye da ita inda kuma suke neman sake fasalin fansho wanda ya dace da yanayin aikinsu, mai adalci da kuma daidai da ayyukansu da tsarin mulki ya basu, sannan kuma da lura da hadarin da suke fuskanta a lokacin gudanar da ayyukansu.
- An Cafke Wadanda Ake Zargin Yi Wa Ma’aikacin PNCH Fashi A Legas
- ‘Yansanda Sun Karyata Jita-jitar Kai Harin Garkuwa Da Mutane A Jami’ar BUK
A takaice dai a cewar Wikipedia, NPF ta samo asali ce tun a shekarar 1879 inda aka kafa kungiyar Hausa Constabulary mai membobi 1,200, sannan aka kafa rundunar ‘yansandan Legas a shekarar 1896.
A farkon shekarun 1900, an kirkiro ’yansandan Arewacin Nijeriya da ’yansandan Kudancin Nijeriya daga sassan Kamfanin Constabulary na Royal Niger Company da Constabulary na Neja Coast. Yayin da a shekarar 1930 aka hade rundunonin ‘yansandan Arewacin Nijeriya da Kudancin Nijeriya suka kafa ‘yansandan kasa na farko a lokacin Turawan mulkin mallaka.
Bayan da Nijeriya ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, rundunar ta sauya suna zuwa rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF), kuma tana da hurumi a fadin Nijeriya. Yana da kyau a sani cewa dokar ‘yansandan Nijeriya an kafa ta a 2020 (‘sabuwar dokar’) wacce ta fara aiki, ta soke dokar ‘yansanda ta 2004.
Ana dara ga dare ya yi, yanzu suna son ficewa daga Tsarin Fansho na Gudunmawa (wato Contributory Pension Scheme-CPS) zuwa Tsarin Fansho Kayyadadde (wato Define Benefit Scheme-DBS)!
Tawayen ‘yanfansho na ‘yansanda
Kafofin yada labarai sun ba da labarin yadda jami’an ‘yansandan da suka yi ritaya a karkashin shirin CPS suka yi wa majalisar dokokin kasar kawanya domin nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu fansho na watanni da dama a ranar 21 ga Mayu, 2024. Da kuma neman a cire su daga tsarin CPS. Ma’aikatan da suka yi ritaya sun wakilci sassan Jihohi daban-daban tare da bayyana irin wahalhalun da suka fuskanta sakamakon gazawar Hukumar Fansho (PenCom) ta kasa wajen biyansu hakkokinsu ba.
An ruwaito cewa wannan bukata tasu ya kai ga shigar da kudirin neman kafa Hukumar Fansho ta ‘Yansandan Nijeriya, wanda majalisar dattawa ta 9 ta zartar a watan Yunin 2023 kamar yadda aka bayyana a shafinsu na D (wato twitter) da kuma kudirin cire rundunar ‘yansanda daga jerin masu karbar fansho ta hanyar CPS wanda dokar PenCom Act 2014 ta ba da izini, yanzu haka wannan kudiri yana gaban Majalisa ta 10 yana jiran daidaito don aiwatarwa tun a watan Nuwamba, 2023 .
Menene CPS?
Dokar sake fasalin fansho ta 2004 da aka kirkira da alama bisa Tsarin Fansho na kasar Chile ce wacce ta kebance Sojoji da ‘yansanda. Fasalin wannan sabon tsarin fansho mai suna CPS, ya kasance ma’iakaci da gwamnati suna bada wani kaso duk wata sanna kuma wanna kudade suna zuwa wajen kamfanoni masu zaman kansu domin sarafawa bisa sharuddan da hukumar PenCom ta gindaya, yayin da alokacin da ma’iakaci ya yi ritaya sai abashi wani kaso daga ciki saura kuma a sarrafa amma biyan shi fansho duk wata daga wannan tanadi nasa.
Wannan tsari na CPS ya kasance mai tabbatar da cewa mai ritaya na samun kudinsa akan kari ba kamar tsarin fansho na DBS wanda gwamnati ke warewa a cikin kudin shekara-shekara na kasafi wanda ba kasafai gwamnati ke biyan fansho ba a kan kari saboda rashin kudi ko kuma rashin nagartaccen tsarin tattalin arzikin kasa.
Gwamnati, ta hanyar Hukumar Fansho (PenCom) ta dage cewa ‘yansanda sun yi girma sosai, cire su daga cikin tsarin CPS zai shafi tattalin arzikin Nijeriya kuma dole ne su ci gaba da kasancewa a cikin CPS yayin da aka kebe Sojoji, NIA da DSS. To amma dai ‘yansanda sun dau alwashin yin kaura zuwa tsarin DBS.
A wani taron jin ra’ayin jama’a na watan Fabrairun 2024 don gyara dokar PenCom, mai daukar nauyin ya dogara da bukatarsa kan cewa Mataimakin Sufeto na ‘yansanda a karkashin shirin fansho na CPS yana zuwa da kusan Naira miliyan 2, yayin da Mataimakin Sufeto na biyu na ‘yansanda ya hauhawa zuwa kimanin Naira miliyan daya, kwatankwacinsu a cikin tsarin DBS kamar Kyaftin a Soja, suna wawurar kimanin Naira miliyan 12, yayin da na DSS ke kwashe kusan Naira miliyan 10.
‘Yansanda, shin maganganun da ke sama, haka ne?
Rushe Sarkokin Fansho
Hukumar NPF na ci gaba da kasancewa babbar hukumar tabbatar da doka a Nijeriya, hana aikata laifuka da gano laifuka, aiwatar da doka, da kare rayuka da dukiyoyi. da dai sauransu.
An balle hukumomi masu sa kayan sarki daga NPF kamar haka:
i. Hukumar kashe gobara ta Nijeriya (Nigerian Federal Fire Serbices) – Asalin sunan ‘yansandan Brigade, an kafa a shekarar 1901 a matsayin bangare, mai suna ‘yansandan Legas, kuma daga baya wata doka ta majalisa ta sake tsarawa a shekarar 1963.
ii. Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (Nigeria Immigration Serbice) – An kirkiro ta a shekarar 1958. Tana da alhakin kula da shige da fice da kuma tsaron kan iyakoki, an kafa ta a shekarar 1963.
Babbar hukumar tsaro a Nijeriya ita ce Rundunar Sojojin Nijeriya (NA), wanda tarihinta ya samo asali ne tun a shekarar 1863 lokacin da Laftanar Glober na Royal Naby ya zabo ‘yan asalin yankin Arewacin kasar su 18 da suka kafa rundunar ‘yansanda da aka fi sani da “Glober Hausas” don kare Kamfanin Royal Niger daga hare-haren ýan ta’adda daga Daular Ashanti da ke makwabtaka da Nijeriya, daga bisani kuma aka kafa rundunar Sojojin Gabar Yammacin Afirka a shekarar 1900.
Wanda aka kirkiro a hukumance a shekarar 1956 aka kafa ta a shekarar 1960, sauran bangarorinta su ne:
a) Rundunar Sojan Sama ta Nijeriya (NAF) -An kafa ta a hukumance a 1964 don tallafa wa NA shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya a Kongo da Tanganyika (yanzu Tanzaniya).
b) Rundunar Sojan Ruwa ta Nijeriya (NN) -Ta samo asali ne daga bangaren sashen Ruwa na Royal Naby da aka kafa a shekarar 1887. Ayyukan ta sun hada da ayyukan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya da Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Cikin Gida, ahalin yanzu da kuma rundunar sojojin ruwa ta Nijeriya. An kaddamar da shi a cikin 1956.
Ma’iakatun da suka yi kama da na aikin Sojoji wadanda suka bayyana a fagen aiwatar da doka sun hada da:
a. Hukumar Kula da Gidan Yari ta Nijeriya (NCS) – wacce a da ake kira Nigerian Prisons Serbice (NPS) kuma ta samo asali ne tun a shekarar 1861 lokacin da aka fara kafa gidajen yari irin na kasashen Turai na Yamma a Nijeriya, canjin suna ya zo a cikin 2019.
b. Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) – An kafa ta a shekarar 1891, c. Code of Conduct Bureau (CCB) – An kafa ta a cikin 1979. d. Hukumar Tsaro ta kasa (SSS) ko (DSS) – An kafa ta a cikin 1986 bayan rugujewar Hukumar Tsaro ta Nijeriya ( wato NSO).
e. Hukumar Leken Asiri ta kasa (NIA) – An kafa ta a 1986 (da ga rusasshiyar NSO).
f. Defence Intelligence Agency (DIA) – An kafa shi a cikin 1986, (da ga rusasshiyar NSO)
g. Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) – An kafa ta a shekarar 1988. h. Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) – An kafa ta a shekarar 1989.
i. Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC) – An kafa shi a shekara ta 2000. j. Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) – An kafa ta a shekarar 2003.
k. Jami’an (Cibil Defence -NSCDC) – An bullo da su a shekarar 1967 lokacin yakin basasar Nijeriya a cikin Babban Birnin Tarayya na lokacin wato Legas kuma aka kafa ta bisa ka’ida tare da fadada wa’adin a 2003.
l. Ko akwai wanda aka manta ba a ambata ba?
Alamu na nuni da cewa an kwafi Kundin Tsarin Mulki na 1999 ne, yana iya zama kalma zuwa kalma daga wani kundin, idan ba haka ba ta yaya NPF ta sami kanta a cikin wannan mawuyacin hali na fansho?
Bari mu ziyarci tarihi. An kafa Hukumar Bitar Ma’aikata ta Udoji a shekarar 1972 ta Gwamnatin Janar Gowon inda ta ba da shawarar sake fasalin ma’aikatan gwamnati. An ba da shawarwari masu tasiri, inda aka karfafa duk dokokin fansho na yau da kullun, fansho na waanda suka je yaki da dai sauransu. Wadannan sun canza albashi da fanshon Ma’aikatan Gwamnati kuma sun samu madogara da ga Dokar Soja mai lamba 102 na 1979 ga ma’aikatan farar hula da Dokar Soja mail amba 103 na fansho na sojoji.
Abin da dokokin suka yi shi ne samar da tsarin fansho na DBS a tsarin Pay-As-You-Go (PAYG), wanda ya dogara ga tanadin kasafin kudi kawai.
Yauwa an zo wurin, yanzu sai mu shiga sashe na 219 na kundin tsarin mulkin shekarar1999 da sashe na 5(1) na dokar sake fasalin fansho na shekarar 2014, wanda ya ba da umarnin kafa wata hukuma da za ta tabbatar da fansho na jami’an soji, daga baya aka kara wasu jami’an tsaro kamar su NIA da DSS da kuma kebe su daga Tsarin Fansho na CPS.
‘Yantar da kudaden fansho
An kaddamar da CPS a cikin 2004, an tsara shi don tabbatar da duk ma’aikatan gwamnati sun sami tabbataccen fansho.
Damuwa da dalilai na rashin barin ‘yansanda su fita daga cikin tsarin fansho na CPS su ne:
Fitar ‘yansanda daga CPS zai haifar da wani gagarumin gibi na kudi a kan gwamnati.
PenCom da NLC sun ba da shawarar habaka gudunmawar gwamnati a cikin tsarin CPS. Za a sami mummunan sakamako ba kawai ga gyaran fansho ba har ma da wasu shirye-shiryen garambawul na gwamnati.
Akwai wata doka (wato White Paper) daga rahoton kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin kasa, kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya wanda ya haramtawa duk wata hukumar gwamnati, baya ga sojoji da jami’an leken asiri fita daga CPS.
Dalilai da suka shafi kudi a cewar PenCom su ne:
1. Zai ci wa gwamnati karin Naira tiriliyan 2 a cikin lamunin fansho akan jami’an ‘yansanda sama da 300,000 dangane da aikin kima na 2021. 2. Jimillar rabon da Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da shi don daidaita kudaden fansho a cikin dokar kasafin kudi ta 2022 shi ne Naira biliyan 125 daga cikin jimlar alhakin fansho na Naira biliyan 577.3 .Wannan jimlar rabon da aka gabatar na fansho na Sojoji, da NIA, da DIA da kuma masu son yin ritaya na ma’ikatun da kudin su ke fitowa daga baitul malin Gwamnatin Tarayya ne. Yayin da adadin kudaden da aka kebe na Sojoji su ne – Naira biliyan 263.3, NIA –Naira biliyan 9.2 na DSS kuma shi ne- Naira biliyan 12.1. 3. Ana ba wa Farfesa damar yin ritaya tare da cikakken fansho idan sun yi aiki na akalla shekaru 20. Lokacin da tanadin CPS din su bai isa ya cika cikakken fansho ba, gwamnati za ta rufe gibin.
4. A karkashin CPS na jami’an ‘yansanda, akwai alhakin da ya kunshi Naira biliyan 213.4 a matsayin hakkin fansho da aka tara da kuma kimanin Naira biliyan 2.2 na gudunmawar fansho na ma’aikata a kowane wata da gwamnati za ta biya. 5. Kimanin kashi 63 na jimlar kadarorin fansho za su shafu ta hanyar hada-hadar kudi, kasuwanni da kasuwannin jinginar gidaje da dai sauransu (wato tiriliyoyin Naira kenan).
Shin Yankewa Ko Fadawa
A karshe: ‘Yansanda, kuna da madogara amma ba a yi tsari mai kyau ba! Masu Gudanar da Asusu na Fansho da Masu Kula da Asusun Fansho, shin akwai dalilin da zai kawo tashin hankali? wata kila! PenCom, akwai mafita amma ba wannan hanyar ba!