Rikicin da ya barke tsakanin Fulani da Gwarawa a kauyen Gurfata da ke karamar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da raunata wasu da dama, yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu bayan da aka kona gidaje 31.
Lamarin wanda ya afku a ranar Talatar da ta gabata, rahotanni sun ce ya samo asali ne daga takaddamar hanya da ta bi ta cikin gonar wani manomi gwari mai suna Sa’adu wacce wani Bafulatani makiyayi mai suna Shaibu Adamu ya yi yunkurin bi da shanunsa ta kan wannan hanya.
- Gwamnati Za Ta Kafa Cibiyoyin Kiwo a Yankuna Shida — Ƙaramin Ministan Noma
- Za A Bude Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Koli Na 20 Na JKS A Watan Oktoban bana
Mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayar da cikakken rahoto game da rikicin a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) a ranar Laraba.
A cewar Makama, rikicin ya fara ne a lokacin da Adamu ya yi yunkurin ratsa gonar Sa’adu, amma manomin ya ki amincewa, inda ya dage sai dai ya bi ta wata hanya ta daban.
Makama ya ce rashin jituwar da ke tsakanin mutanen biyu ta kai ga doke-doke.
“Nan da nan, al’amura suka kara kazanta yayin da dan uwan makiyayi Shaibu, Adamu Ibrahim, ya kai wa wani manomi dan garin hari, Dahiru Yakubu, da adda.
“An garzaya da Yakubu zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, inda daga baya ya rasu,” In ji Makama.
Labarin mutuwar Yakubu ya haifar da harin ramuwar gayya daga fusatattun matasan Gwari, inda suka far wa Fulani a kauyen, inda suka kona gidaje 31 tare da raunata akalla mutane uku.
Daga baya an tura sojoji tare da wasu jami’an tsaro zuwa yankin domin kwantar da tarzoma da kuma dawo da zaman lafiya.
“Hukumomi sun yi kira da a samar da zaman lafiya tare da yin kira ga al’ummomin biyu da su yi hakuri, a halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin sasanta bangarorin biyu da kuma hana barkewar rikici.”
Ya kara da cewa har zuwa yau Laraba al’amura sun koma kamar yadda aka saba duk da cewa har yanzu ana zaman dar-dar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp