Rikicin Masarautar Kano ya dauki wani salo na daban, yayin da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce magoya bayansa sun yi kokarin kare kansu ne a rikicin da ya barke a ranar Lahadi a fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
A ranar Lahadin da ta gabata ce magoya bayan Sarki Sanusi II da na Sarkin Bayero suka yi artabu a fadar Sarki Sanusi na Kofar Kudu, lamarin da gwamnatin jihar ta bayyana a matsayin abin takaici, inda ta bayyana cewa an jikkata wasu ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
- EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
A wata sanarwa da sashen yada labaran Masarautar Kano ta fitar tun farko mai dauke da sa hannun Sadam Yakasai, ta ce Sarki Sanusi yana wajen fadar a lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce, “Sun fasa kofar ne suka far wa masu gadin, inda suka jikkata wasu daga cikinsu, suka farfasa motocin ‘yansandan da ke cikin fadar, da gangan Aminu ya bi ta hanyar fadar sarki maimakon ya bi hanyar da ta dace daga Koki zuwa Nassarawa, sai ‘yan bindigar suka yanke shawarar kai hari Gidan Rumfa.”
Sai dai da yake mayar da martani kan lamarin na ranar Lahadi, Sarki Ado Bayero ya ce a jiya magoya bayansa sun yi hakan ne domin kare kansu.
Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai.
Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta musu dakile harin.
A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin Bayero ya taba bi ta wannan hanyar ba.
“Bayan isowarmu daga gidan Dantata domin jaje, wasu matasa sun mamaye titin da duwatsu da makamai a Kofar Kudu.
“Lokacin da muka isa Kofar Kudu, sai suka fara jifan mu, amma aka yi sa’a, mun yi nasarar fatattakar su zuwa cikin gida, kuma Sarkin ya wuce cikin nasara ba tare da wani ya samu rauni ba,” in ji shi.
Uba ya tabbatar da korar magoya bayan Sarkin Bayero daga fadar, inda ya ce sun samu korafe-korafe daban-daban a kan lamarin.
Sarakuna biyu a gari daya
Rikici ya barke a Masarautar Kano biyo bayan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Maido da masarautun ya biyo bayan sake duba dokar Masarautar da ta samar da karin masarautu guda hudu.
An dai kalubalanci matakin a gaban kotu, inda Aminu Ado Bayero ya ki amincewa ya yi murabus daga karagar mulki. Ya ci gaba da zama fadar Nasarawa a karkashin kulawar jami’an tsaro.
A ranar 23 ga Mayu, 2024, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sanusi Sarkin Kano. Tun shekaru hudu da suka gabata ne tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige Sanusi daga mukamin sarki, wanda ya jagoranci masarautar Kano da kuma tsige Sanusi daga karagar mulki.
Wadanda aka kora daga fadar sun koka da makomarsu
A halin da ake ciki, daya daga cikin wadanda aka kora daga fadar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya jefa ta da ’yan uwanta cikin rudani inda aka tilasta musu barin fadar.
Ta yi zargin cewa mutanen da suka fatattake su sun fito ne da ‘yan daba, inda suka cire rufin kofofi da tagoginsu, suka kuma umarce su da su bar fadar cikin sa’o’i 24.
Ta kara da cewa mutanen sun zazzagi wadanda ba su son Sarki Sanusi ko kuma masu biyayya ga Sarki Bayero tare da yin barazanar cutar da duk wanda ya ki amincewa da korarsu.
“Wasu mutanen da ke Kofar Kwaru an riga an ba su sanarwar a ranar Lahadi da tsakar dare don su fice ranar Litinin, yayin da mutane irin mu suka shiga halin rashin tabbas a ranar Litinin.
“An dauki matakin ‘yansanda kafin su ba mu damar kwana har zuwa yau (Talata), amma a halin yanzu, mun yi tattara kayanmu domin komawa ga wasu ‘yan uwa,” in ji ta.
Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shiga tsakani, inda ta koka da rashin taimakon su.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta ce ta kama wasu mutum hudu da ake zargi da hannu a harin da aka kai a fadar Sarki Sanusi da ke Kofar Kudu a cikin birnin Kano ranar Lahadi.
Hakan ya biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 16, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da magoya bayan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, a fadar Sarki Sanusi na Kofar Kudu.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya shaida wa manema labarai a Kano cewa wadanda ake zargin suna hannun ‘yansanda kuma suna kan bincike.
A cewarsa, kwamishinan ‘yansandan jihar, Ibrahim Bakori, ya kafa kwamitin da zai binciki fadan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp