Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarnin hana kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP cire Jakada Umar Illiya Damagum daga muƙaminsa na riƙon shugabancin jam’iyyar.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke wannan hukunci a yau Juma’a, inda ya dakatar da duk wani yunƙuri na tsige Damagum daga mukaminsa.
- Na Yi Wa Yara 80 Kaciya Cikin Shekara 17 Da Na Yi A Duniya – Budurwa Wanzamiya
- Zaben Edo: PDP Ta Lashi Takobin Zuwa Kotu
Wannan hukuncin ya biyo bayan wasu al’amuran da suka faru a baya, inda Damagum da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, suka samu dakatarwa daga wani ɓangare na kwamitin aiki na ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP. Matakin kotun na nufin tabbatar da tsarin shugabanci na yanzu a jam’iyyar duk da rikice-rikicen cikin gida.