Kallo ya sake komawa kotu dangane da rikicin sarautar Kano, yayin da aka ci gaba da saurarar karar da aka shigar kan rushe masarautu da tsige sarakunansu.
A bangaren Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda yake da goyon bayan gwamnatin Jihar Kano ya ci gaba da shimfida mulki daga fadar gidan Dabo, inda yake samun kariyar gwamna da jami’an Karota, ‘yan tauri da jami’an sa-kai.
Yayin da Sarkin Aminu Ado Bayero ke zaman tasa fadar a gidan sarki na Nasarawa, wanda shi kuma ake hangen jami’an tsaron soja da ‘yansanda ke tsaronsa.
Tun bayan sake dawowar Sarki Muhammadu Sanusi II, sarkin ya fara limancin sallar Juma’a, sarkin ya yi sallah a masallacin Juma’a da ke fadar Gwmnatin Jihar Kano a makon farko bayan dawowarsa, haka zalika a makon da ya gabata ya jagoranci sallar juma’ar a babban masallacin sarki na Kano.
Abin da ke ci gaba da kai komo a zukatan Kanawa shi ne, yadda kotuna uku suka bayar da umarni daban-daban kan al’amarin. Inda kotun farko wadda babbar kotun tarayya ce da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga fadar gidan Rumfa.
Kotun ta kuma umarci ‘yansanda da su tabbatar an ba Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero duk wani hakki da alfarmar da ta kamata a ba shi.
Mai shari’a S. A. Amobeda wanda ya bayar da wannan umarnin ya bayyana cewa an yi wannan hukunci ne domin tabbatar da adalci da kuma wanzar da zaman lafiya a Jihar Kano.
Sai dai kuma wata kotun daban ta hana jami’an tsaro korar Sarki Sanusi II, sakamakon umarnin da Mai Shari’a, Amina Adamu Aliyu ta babbar. Kotun Kano da ke zamanta a titin Miller, ta hana ‘yansanda, hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da sojoji korar Sarki Sanusi II daga fada.
Sarki Sanusi II ne ya shigar da karar tare da masu nadin sarkin Kano hudu, wanda suka hada da Madakin Kano, Yusuf Nabahani da Makaman Kano, Ibrahim Sarki Abdullahi da Sarkin Bai, Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Maituta, Bello Tuta.
Wannan hukunce-hukunci ta kara dagula lamura tsakanin Sarki Sanusi II da Aminu Bayero wadanda suke fafatawa a neman kujerar sarautar Kano. Rigimar dai ta janyo zanga-zangar a tsakanin magoya bayansu a sassan Jihar Kano.
Sai dai kuma sakamakon yajina kungiyar kwadago ta tsunduma ranar Litinin da ta gabata, wadda ita ce ranar da ake sa ran fara sauraron waccan kara ya sa dole an dage sauraron karar har zuwa ranar Alhamis.
A wani kokarin na kamo bakin zaren, Alkalin-alkalan Nijeriya ya kira manyan alkalan Kotun Tarayya da ke Jihar Kano kan bayar da hukunci masu cin karo da juna, domin warware dambarwar Masarautar Kano.
Sai dai duk wancan umarnin na kotu, an hangi akalla hakimai 40 suka yi mubayi’a ga mai martaba Sarkin Sanusi II.
Kano dai na da hakimai 65, wanda mubayi’ar 40 ga Sarkin Kano Sanusi II na nufin ya samu rinjaye goyon bayan hakiman kan wadanda suka goyi bayan Aminu Ado Bayero. Sai dai Bahaushe na cewa, ‘ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.’