Ga dukkan alamu har yanzu da sauran rina a kaba game da rikicin siyasar da ta turnike Jihar Ribas bisa yadda masu ruwa da tsaki na jihar suka yi fatali da sabon sulhun da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi a tsakanin Gwamna Fubara da Ministan Abuja, Nyesome Wike.
Kungiyar Dattawa da Shugabannin Jihar Ribas (RELF) ta ce kudurori da umarnin da suka biyo bayan sulhun da aka yi a ranar Litinin sun yi hannun riga da umarnin da kotu ta bayar kan lamarin.
- Kamfanin Man Nijeriya Ya Sa Hannu Kan Fasahar Gano Sinadarin Methane
- Yawan Sinawan Da Suka Rasu Sakamakon Girgizar Kasa Ya Karu Zuwa 148
Kungiyar ta RELF ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Ribas, Cif Rufus Ada-George ya karanta wa manema labarai, ta bayyana cewa yarjejeniyar da aka yi ta kuma saba wa kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999, wanda shugaban kasar ya rantse za iyi aiki da shi.
“Mun yi taron gaggawa na kungiyar Dattawa da Shugabannin Ribas da aka gudanar a ranar 19 ga Disamba, 2023 don mayar da martani kan tsoma baki da umarnin da Shugaban Kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya bayar kan rikicin siyasar Jihar Ribas… Sai dai mun rasa ina aka dosa, shin abin da Tinubu ya yi ya warware matsalar ce ko dai ya kara ta’azzara ta
“Umarnin ya wancakalar da kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya baki daya saboda yunkurin soke umarnin kotu na amincewa da Rt. Honorabul Edison Ehie a matsayin shugabar majalisar tare da ba da umarnin cewa sauran ‘yan majalisar ne ke kawo cikas ga harkokin majalisa.
“Haka ma wannan umarni ya ci karo da ka’idar rabon madafun iko, musamman yadda ya shafi bangaren shari’a. Shin shugaban kasa ko hukuncin gwamnatinsa zai iya rusa hukuncin hukuncin kotu?
Wannan yana nuna bangaranci wanda ke lalata tsarin mulkin demokuradiyya, bin doka da kyakkyawan shugabanci.
“Tanade-tanaden yarjejeniyar sun nuna goyon baya ga Cif Barr. Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya da kuma cin mutuncin gwamna, Siminialayi Fubara da mutanen Ribas nagari.” In sanarwar.
Hakazalika, kabilar Ijaw a karkashin jagorancin Edwin Clark ta ce hawainiyar shugaban kasar ta kiyaye ramar Gwamna Fubara na jihar.
“Mun shirya wa duk irin abin da zai iya biyo baya a rikicin Jihar Ribas. Kuma za mu yi fito-na-fito da duk wani yunkuri na mayar da dan kabilar Ijaw, Siminialayi Fubara da aka zaba a matsayin gwamna ya zama marainin Nyesome Wike wanda bisa goyon bayan da ya samu daga Shugaba Bola Tinubu, yake bugun kirjin cewa duk wanda ya taba tsarin da ya kafa zai gamu da tutsunmu.
“Za mu tafi kotu domin nuna rashin amincewar da irin cin kashin da ake mana ta hanyar da doka ta shimfida. Kuma muna kira ga matasa da suka fusata kan abin da yake faruwa su kai zuciya nesa, domin za mu magance lamarin”, in ji Clark a wani taron manema labarai.
Har ila yau, kabilar ta ce sulhun da aka yi, an yi kashin dankali kuma ya saba wa dokokin tsarin mulkin kasa, don haka ba za su lamunta ba.
A farkon makon nan ne dai Tinubu ya gayyaci bangarorin da ke gaba da juna a fadarsa da ke Abuja, inda suka rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu tsakanin Wike da magajinsa Fubara.
Rikicin siyasar jihar ya kara kamari ne a makon da ya gabata, yayin da ‘yan majalisar dokokin jihar 27 da ke biyayya ga Wike suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya sa ‘yan majalisar da ke biyayya ga Gwamna Fubara suka bayyana kujerunsu a matsayin wadanda babu kowa.
Wutar rikicin ta kara ruruwa har ta kai ga murabus din kwamishinoni tara na gwamnatin Fubara masu biyayya ga Wike.
Sai dai kuma, biyo bayan sabon sulhun da Tinubu ya yi, yarjejeniyar ta umurci Gwamna Fubara ya janye kararrakin da ya shigar a kotuna, sannan ta umarci majalisar dokokin jihar ta yi watsi da batun tsige gwamnan.
Haka kuma ta bayar da umarnin a amince da shugabancin Amaewhule a majalisar dokokin jihar, kana Gwamna Fubara ya sake gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar da Amaewhule ke jagoranta.
Sannan an amince tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Ribas, Rt. Hon. Martin Amaewhule da mambobi 27 da suka fice daga PDP su koma kujerunsu tare da biyan su hakkokinsu.