An dawo da kashin karshe na ‘yan Nijeriya da suka makale a rikicin kasar Sudan, sun taso ne daga filin jirgin sama na Port Sudan.
Kawo yanzu gwamnatin tarayya ta dawo da ‘yan Nijeriya 2,518 gida.
Wannan rukunin sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a ranar Asabar, 13 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 6:36 na yamma a cikin jirgin kamfanin Tarco.
Jirgin dai ya kwaso ‘yan Nijeriya mutum 147 wanda wannan shi ne na biyu da kamfanin ya yi kan jigilar ‘yan Nijeriya. Jirgin na farko ya kwaso mutane 125.
An bayyana hakan ne a wata sanarwar hadin guiwa a ranar Lahadi, wanda Amb. Janet Olisa, Daraktar Kula da Ofishin Babban Sakatare, Ma’aikatar Harkokin Waje (MFA) da Dr. Nasir Sani-Gwarzo, Babban Sakatare a Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Tarayya da Ci gaban Jama’a (FMHADMSD) suka fitar.
Dukkansu sun ce kwasu ‘yan Nijeriya daga Sudan yana daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa kada a bar wani dan Nijeriya da ke neman tsira daga rikicin kasar Sudan a baya.