• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Uba Sani Da El-Rufa’i Ya Dauki Sabon Salo

by Rabi'u Ali Indabawa
9 months ago
Uba sani

Rikicin da ake tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kaduna da gwamna mai ci Uba Sani na ci gaba da daukar sabon salo, inda dukkaninsu ke kai wa juna hare-hare cikin kalamai.

Gwamna Sani a wata hira da ya yi a gidan talabijin na kasa ranar Litinin ya yi kakkausan suka ga abin da ya kira gamayyar ‘yan siyasa da suka taru kwanan nan don sukar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

  • ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 5 A Kaduna.
  • Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna 

A cikin hirar, gwamnan ya zarge su da adawa da gwamnati don neman mulki kawai maimakon samar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen da ke addabar Nijeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa babu daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar da zai iya adawa da manufofin dimokuradiyyar Tinubu, yana mai jaddada cewa shugaban ya yi gwagwarmaya kuma ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da dimokradiyya.

Idan dai ba a manta ba a makon da ya gabata ne Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, na cikin wasu manyan ‘yan siyasa da suka hallara a wani taro a Abuja, inda suka caccaki gwamnatin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki.

LABARAI MASU NASABA

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Gwamna Sani ya bayyana zargin da kungiyar ta yi a matsayin maras tushe, yana mai jaddada cewa “Mafi yawan ‘yan siyasar da ke irin wadannan kalamai na iya zama suna magana da kansu ne kawai,” in ji shi. “Mun kasance a cikin jam’iyya daya a wani lokaci, kuma dole ne in ce na yi mamakin abin da suka yi.”

Ya kara da cewa kawancen ba shi da wata hujjoji ta gaskiya kan ikirarin nasu.

“Fito da zarge-zarge ba tare da hujja ba, wani yunkuri ne kawai na kawar da hankulan ‘yan Nijeriya,” in ji gwamnan.

“Yawancin wadannan ‘yan siyasa sun rike mukamai a gwamnati kasa da shekaru biyu da suka gabata. Me suka yi a lokacin da suke kan mulki?”

Ya nuna shakku kan sahihancinsu, yana mai nuni da cewa yakinsu sun yi ne kawai a lokacin suna kan mulki.

“Yan Najeriya suna fa fahimta, kuma sun riga sun san wadannan ’yan siyasa ba wai suna fada da Tinubu ba ne saboda sun fi shi sanin abin da ya fi dacewa da su, a’a sun samu dama a baya amma me suka yi?

Gwamna Sani ya kara da cewa a kwanakin baya wasu ‘yan siyasa sun yaba wa Shugaba Tinubu amma sun canja ra’ayinsu bayan barin gwamnati.

“Mafi yawansu suna zaune a teburi daya da mu, suna yakar Tinubu saboda mun yi imanin cewa shi ne mutumin da ya fi dacewa ya ciyar da kasar nan gaba,” in ji shi. “Mene ne shaidar dimokuradiyya, idan zan iya tambaya? Me suka yi domin ciyar da dimokuradiyya gaba a Nijeriya?” Ya tambaya.

A martanin da El-Rufai ya mayar a shafinsa na D, ya caccaki gwamnan, yana mai cewa, “Mutanen Jihar Kaduna za su yi hukunci.”

El-Rufai, a cikin shafinsa na D mai taken “Kaduna Update,” ya ce gwamnan yana “borin kunya ne da rudani” a kowace rana.

“Ina mamakin dalili, ko da yake na tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ‘ramawa’ kura aniyarta, ya bai wa Kaduna tallafin da ya haura Naira biliyan 150, a cikin watanni 18 da suka gabata, yanzu ya bayyana komai.”

“Ta kowane hali suke kare Asiwaju don samun kudi bisa sharadi. Asiwaju ya amfana da ku. Al’ummar Jihar Kaduna za su yi hukunci a daidai lokacin da ya dace, kamar yadda ya rubuta.

A wani labarin kuma, El-Rufai ya ruwaito cewa, tsohon firaministan kasar Birtaniya Tony Blair na cewa a wani lokaci da ya gabata: “ Cikin kasashe masu tasowa, inda mutane ke gwagwarmayar sanya abin da za su sa a bakinsu, zuwa makaranta, samun ilimin kiwon lafiya na yau da kullum, samar da rayuwa ba sana’a ba, (ayyukan zamantakewa) bayarwa na iya zama bambanci tsakanin rayuwa da mutuwa; ko akalla bambanci tsakanin rayuwa mai cike da bege da wacce ta sava da hakan.

“Su (‘yan kasa) suna son a magance matsalolin da ke shafar rayuwarsu ko a rage su. Suna son ingantacciyar rayuwa, ingantaccen kiwon lafiya, ilimi da tsaro.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta
Siyasa

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa
Siyasa

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

October 22, 2025
Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya
Siyasa

Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

October 21, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.