An kashe wani matashi dan shekara 15 mai suna Saidu Udu a wani rikici da ya barke a garin Minna na Jihar Neja a ranar Asabar.
Jami’an ‘yansanda sun cafke mutum biyar da ake zargi da yunkurin tserewa daga wurin.
- Sin Ta Dauki Matakin Martani Kan Kamfanonin Makamai Na Amurka
- Fiye Da Kaso 80 Na Kamfanonin Sin Sun Fadada Zuba Jari A Waje A 2024
Rundunar ‘yansandan Jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa jami’an sintiri nasu sun kai dauki amma tuni ‘yan dabar suka gudu.
Kakakin rundunar ‘yansandan, Wasiu Abiodun, a wani sakon WhatsApp da ya aike wa PUNCH Online, ya ce: “A ranar 21/12/2024 da misalin karfe 11:30 wasu ‘yan Daba daga yankin Gurgudu da ke Maitumbi da Kwari-Berger sun far ma juna, lamarin da ya kai ga mutuwar wani Saidu Udu, mai shekaru 15, daga Gurgudu. Tawagar ‘yansanda da ke sintiri daga sashin Maitumbi ta koma wurin da lamarin ya faru, amma ‘yan Dabar sun tsere. An kai wanda aka an tadi da wanda ya shafa zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
“A wani samame da aka kai a yankin, an kama wasu bata gari biyar. A yanzu haka ana gudanar da bincike, kuma ana ci gaba da kokarin kamo sauran ‘yan Dabar da suka tsere.”
Rikicin, wanda rahotanni suka ce ya hada da ’yan iska fiye da 50, an ce ya samo asali ne daga rashin jituwa kan rabon kudaden Kirsimeti da ake zargin wani da ba a tantance ba ya ba su.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan Dabar dauke da wukake, sun rikide zuwa tashin hankali, wanda ya kai ga caka wa Udu wuka a ciki.
Wani magidanci mai suna Malik Nurudeen ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce, “’Ya’yan unguwar nan kullum suna zuwa suna yi mana barazana, amma a yau sun haura 50, da farko mun dauka kungiya daya ce, amma daga baya muka gano wasu kungiyoyi ne guda biyu. Daga gardamarsu, ya bayyana a fili cewa sun karbi kudin Kirsimeti daga wani amma sun kasa yarda da tsarin rabon kudin.
“Sun fara yi wa juna barazana da makamansu har sai da aka caka ma daya daga cikin su wuka, sannan kowa ya fara gudu,” in ji shi
.
Mazauna garin sun koka da yadda ake samun karuwar tashe-tashen hankula a Minna, tare da yin arangama akai-akai da ke barin wadanda abin ya shafa suka jikkata, ko kuma a kashe su.
Duk da kokarin da ‘yansanda suka yi na dakile ayyukan ‘yan iskan da aka fi sani da ‘Yan Daba (Area Boys), ‘yan ta’adda na ci gaba da addabar garin.
An bayar da rahoton cewa an kashe mutane da dama ko kuma raunatawa a yayin da ’yan ta’addan suka yi arangama, wadanda su kan kaucewa kamawa tare da ci gaba da munanan ayyukansu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shawulu Danmamman, ya bayar da tabbacin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan.