Sufeton Janar na ‘yansandan Nijeriya, IG Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayyana harin da wasu jami’an sojojin Nijeriya su ka kai hedikwatar ‘yansandan Jihar Adamawa a kwanan baya, da cewa kamar rundunar na yaki da jami’an tsaron sojojin.
Adeolu, ya bayyana haka ne a Yola a ranar Talata, a ziyarar da ya kai jihar domin jajanta wa iyalan Insifekta Jacob Daniel, dan sandan da ya rasa ransa, sakamakon harin da sojojin su ka kai a ranar 24 ga watan Nuwamba 2023.
- Kofin Duniya Na Matasa ‘Yan Kasa Da Shekaru 17: Kasar Faransa Ta Tsallaka Zagayen Karshe
- Xi Ya Jaddada Bukatar Raya Tsarin Shari’a Mai Nasaba Da Ketare
Ya ci gaba da cewa “Hari ne da ya yi kama da na ‘yan bindiga ko ‘yan Boko Haram, wannan harin abin Allah-wadai ne da bakin ciki da takaici, alhali ba yaki ‘yansanda ke yi rundunar soja ba, kuma ko ita rundunar sojan ba ta ji dadin abin da ya faru ba” in ji Kayode.
Ya kuma shaida wa jami’an ‘yansandan irin matakan da aka dauka domin warware matsalar.
Ya ce “wannan arangamar da aka samu tsakanin ‘yansanda da sojoji, manyan jam’an tsaro da hukumomi a matakin kasa sun warware ta”.
Haka kuma shugaban ‘yansandan na kasa, ya bukaci jami’an da su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaron lafiya da dukiyar al’umma kamar yadda su ka saba.
Ya kuma bada tabbacin bin kadun kisan da aka yi wa dan sandan.
Ya kuma yaba wa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, bisa shiga batun da taimak awa iyalan jami’an da su ka rasa ransu a lokacin rikicin.
Da yake maida martani gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya gode da matakin da shugaban ‘yansandan na kasa ya dauka kan karin kudaden kyautata yanayin aiki ga jami’an ‘yansandan, ya ce matakin zai haifar da kyakkyawan sauyi a bangaren jami’an tsaro.
Gwamnan ya kuma bukaci kafa makarantar bada horo ga jami’an ‘yansandan a Mbamba a Karamar Hukumar Yola ta Kudu, da cewa hakan zai inganta aikin da samar da tsaro a jihar da kasa baki daya.