Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin sauke nauyin bashin kamfanin rarraba wutar landarki da ke Abuja (AEDC), domin gudun yanke wutar lantarkin fadar shugaban kasa.
Wannan umurni ya zo ne a daidai lokacin da hukumar AEDC ta yi barazanar yanke wutar lantarkin fadar shugaban kasa da wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati 86 saboda bashin fiye da naira biliyan 47 da hukumar wutar lantarki na yankin Abuja ke binsu.
- ‘Yan Nijeriya Ku Ba Wa Tinubu Ƙarin Lokaci Zai Magance Matsalolin Nijeriya – Gowon
- Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kashe Jagoran ‘Yan Ta’adda Boderi
Sanarwar da hukumar wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya nuna cewa, ana bin fadar shugaban kasa Naira miliyan 923.9; ana bin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro naira biliyan 95.9; mai’aikatar babbar birnin tarayya Naira biliyan 7.57, yayin da ake bin ma’aikatar wutar lantarki naira miliyan 78.
A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, AEDC ta ce ta wallafa sunayen hukumomin gwamnatin ne wadanda ake binsu bashin kudaden wutan lantarki saboda kokarin da aka yi a baya na ganin sun mutunta hakkokin, amma hakan bai haifar da sakamakon da ake bukata ba.
AEDC ta yi barazanar katse wutan lantarkin hukumomin gwamnati har guda 10 wadanda suka gaza biyan bashinsu.
“Hukumar AEDC ta bai wa wadannan hukumomin gwamnati wa’adin gwanati 10 tun daga lokacin da aka wallafa sunaye har zuwa ranar Laraba 28 ga Fabrairun 2024, idan har ba su biya ba, za a yanke musu wutan lantarki har sai sun biya basukan da ake binsu,” in ji sanarwar.
Rahotanni sun nuna cewa babban ofishin hafsan tsaro da barikokin sojoji ne suka fi yawan bashin, wanda ake bin su naira biliyan 12, sai ma’aikatan kudi da ake bin naira biliyan 5.43, da kuma gidan gwamnatin Jihar Neja da ke Abuja da ake bin sa bashin naira biliyan 3.45.
Kazalika, karamar ma’aikatar man fatur ana bin ta naira biliyan 2.13, ma’aikatan ilimi ana bin ta naira biliyan 1.82, Babban Bankin Nijeriya ana binsa naira biliyan 1.56, hukumar ‘yansandan Nijeriya ana bin ta naira biliyan 1.38, bankin duniya ana binsa naira miliyan 17.60, gidan gwamnatin Jihar Ribas da ke Abuja ana binsa naira miliyan 15, gidan gwamnatin Jihar Ogun da ke Abuja ana binsa naira miliyan 1.51, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ana binta naira miliyan 291, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ana binta naira miliyan 75, hukumar yaki da zambar kudade ana binta naira miliyan 60.55, hukumar kula da jiragen saman Nijeriya ana binta naira miliyan 846 da kuma ma’aikatan kula da ‘yan bautar kasa ana binta naira miliyan 56.38.
Sauran sun hada da ma’aikatun lafiya da yada labarai da harkokin kasuwanci da kasafi da tsare-tsaren kasa da noma da sadarwa da al’adu da yawon bude ido da sufuri da ma’adanai da kimiyya da muhalli da harkokin mata da shari’a da kuma kwadago duk suna cikin wadanda ake bi bashin wutan lantarki.
Haka kuma akwai ofisoshin gwamnoni da ke Abuja da suka hada da na Legas, Edo, Kaduna, Anambra, Ondo, Delta, Bayelsa, Zamfara, Inugu, Nasarawa da kuma Katsina na daga cikin wadanda hukumar wutar lantarki a Abuja ke bin bashi.
AEDC ta ce daga cikin wadanda take bin bashin har da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, shugabannin hukumar Kwastom, hukumar tattara haraji ta kasa, mai tsawatarwa na majalisa, ofishin ma’aikan tsaro, shalkwatan kungiyar ECOWAS, alkalin-alkalai na Abuja, COREN da dai sauransu.
Rahotanni dai sun bayyana cewa ministan wutan lantarki, Adelabu wanda AEDC ke bin ma’aikatansa bashi, ya bayyana cewa rashin biyan kudin lantarki yana daya daga cikin manyan matsaloli da ke addabar bangaren wutar lantarkin Nijeriya.
Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun Adelabu, Bolaji Tunji, ya bayyana cewa ministan ya biya bashin da ake binsa tun lokacin da ya shiga ofis.
A cewar Tunji, Adelabu ya dade yana korafin cewa rashin kudade na kawo cikas ga bangaren wutan lantarki bai kamata ya rika wa hukumar AEDC bashin kudin wuta ba.
Ya kara da cewa duk wata zai ministan ya biya kudin wutan lantarki. Tunji ya ce Adelabu ya gaji wannan bashin ne daga tsohon ministan da ya gada.